Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun kashe wasu matafiya a kan hanyar Abuja

Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun kashe wasu matafiya a kan hanyar Abuja

Labarin da muke samu yanzu na sanar damu cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun kashe matafiya a Kotonkarfe ta jihar Kogi dake hanyar Lokoja-Abuja.

Wani wanda wannan al’amarin ya faru a gabansa ya ce, ‘yan bindigan kwanton bauna suka yi a saman hanyan gabanin su budawa wata mota kirar Sharon wuta wadda ta nufi Abuja daga Fatakwal.

KU KARANTA:Gwamna Fintiri ya nada kwamitin gudanarwa na Jami’ar Adamawa

A sakamakon harbin duka fasinjojin dake cikin motar suka mutu. Haka kuma wani ganau wanda ya samu kubuta da kyar ya ce a yammacin ranar Talata da karfe 5:58 ne wannan abu ya faru.

Da yake bada labarin lamarin ga wakilin jaridar Daiily Trust wanda abin ya faru a kan idonsa ya ce: “A daidai lokacin da motar Sharon din ta hangi ‘yan bindigan wadanda ke sanye da tufafin sojoji ta yi koarin juyawa amma ina, saboda harbin ‘yan bindigan ya fasa tayoyin motar.

“Sai a wannan lokacin ne muka tabbatar cewa ba sojoji bane kuma muke tsammanin cewa masu satar mutane ne. An harbi direban motar a kafada wanda harsashi ya ratsa ya je cinma wani fasinja a kai.” Inji wani ganau.

Ya cigaba da cewa, “A hankali muka lallaba muka isa ofishin ‘yan sanda dake Gegu-Beki inda jami’an dake aiki a wurin suka rakamu zuwa Babban Asibitin Kotonkarfe kafin daga bisani mu je FMC Lokoja.

“Direban da harsashi ya shafesa an tura shi zuwa Asbitin kasa dake Abuja, yayin da wasu mutum biyu dake zaune a bayan motar an tura su zuwa Asibitin koyarwa na Jami’ar Ibadan sakamakon raunin da harsashi yayi masu.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel