Yan sanda sun kashe mutum 2 sannan suka lalata sansanin masu garkuwa da mutane a Bauchi

Yan sanda sun kashe mutum 2 sannan suka lalata sansanin masu garkuwa da mutane a Bauchi

Rundunar yan sanda reshen jihar Bauchi ta kashe masu garkuwa da mutane biyu tare da tarwatsa sansanin su a karamar hukumar Alkaleri, sa’o’i 48 bayan yan sandan sun kashe mutum daya a wani lamari makamancin haka a kauyen Miri a karamar hukumar Bauchi dake jihar.

A wani jawabin da kakakin rundunar, DSP Kamal Datti Abubakar ya sa hannu a Bauchi, ya bayyana cewa a lokacin da rundunar take gudanar da ayyukanta ne ta kama miyagun makamai.

Jawabin ya kara da cewa an kai masu garkuwa da mutanen biyu wadanda suka ji rauni zuwa asibtin koyarwa na Tafawa Balewa don samun kulawa inda daga bisani likita ya tabbatar da mutuwarsu.

Kayayyakin da aka gano a lokacin aikin sun hada da bindigogi AK-47, alburusai goma sha daya da mashina hudu.

Jawabin ya bayyana cewa babu wanda yaji rauni daga tawagar yan sanda ko daga cikin al’umma masu hidima, inda ya kara da cewa ana gudanar da bincike da kuma kokari don ganin an kama yan fashin da suka tsere.

KU KARANTA KUMA: Yan majalisar dokokin jihar Sokoto na APC 2 sun lallasa yan PDP a kotun

Rundunar reshen ta bukaci karin goyon baya daga mutanen jihar da samar da bayanai ga yan sanda da sauran hukumomin tsaro akan yan fashi da sansanin yan fashi a cikin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel