Gwamna Fintiri ya nada kwamitin gudanarwa na Jami’ar Adamawa

Gwamna Fintiri ya nada kwamitin gudanarwa na Jami’ar Adamawa

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya nada kwamitin gudanarwa na Jami’ar Jihar Adamawa dake Mubi wato ADSU.

Daraktan kula da lamuran yada labaran gwamnan, Mr Solomon Kumangar ne ya fitar da wannan sanarwa ranar Laraba 25 ga watan Satumba, 2019 a Yola babban birnin jihar Adamawa.

KU KARANTA:Salon yaudara ne saboda zaben 2023 dalilin da yasa El-Rufai ya sanya dansa a makarantar gwamnati – Shehu Sani

A cikin sanarwar tasa, Solomon ya ambaci Auwal Tukur a matsayin shugaban kwamitin wanda ke da mambobi bakwai.

Saura mambobin kwamitin sun hada da; Zira Maigadi, Kashim Nijdda, Zubairu Gabdo da kuma wasu wakilan ma’aikatar shari’a da ilimin gaba da sakandare na jihar.

Haka kuma ya kara da cewa wannan kwamitin zai soma aiki kai tsaye ba tare da bata lokaci ba. Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ne ya fitar da wannan labari.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta takwas, Shehu Sani ya soki sanya Abubakar makarantar gwamnati da El-Rufai yayi.

A cewar sanatan wannan abu ba komi bane in banda yaudara saboda zabe mai zuwa na shekarar 2023. Ya kuma kara da cewa indai maganar wasan kwaikwayone daga gwamnan ba yau muka soma gani ba.

Wadanda ba cikin Kaduna suke za su yi tunanin gwamnan yayi wani abin birgewa alhali ba su san irin yanayin da makarantun gwamnatin Kaduna ke ciki ba, a cewar Shehu Sani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel