El-Rufai zai samar da jiragen sama guda 2 domin jigilar fasinja zuwa Abuja

El-Rufai zai samar da jiragen sama guda 2 domin jigilar fasinja zuwa Abuja

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya rattafa hannu kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin jahar da kamfanin jirgin sama ta Quorum Aviation Ltd, QAL, domin samar da jiragen sama guda 2 da zasu yi safarar Kaduna zuwa Abuja, Kaduna zuwa Legas.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa a cikin yarjejeniyar da aka shiga, kamfanin za ta yi safarar jirage sau biyu a rana, kuma sunan da za’a kira jiragen shi ne ‘Boku Air’.

KU KARANTA: Yansanda sun kama wasu daliban jami’a 8 dake fashi da makami

Majiyar Legit.ng ta ruwaito, Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa yana da tabbacin wadannan jirage zasu rage rububin da jama’a ke yi na bin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja. “Ina da tabbacin kamfanin jirgin zaizo da amfani sosai.

“Don haka nake kira ga yan kasuwa maza da mata dasu ci gajiyar wannan tsarin tafiya a jirgin sama, mun kuma gode ma kamfanin QAL bisa gamsuwa mu kulla wannan yarjejeniya dasu, don haka zamu mika musu titin jirgin da muka gina, muka kuma sanya kayan aiki da kudinmu.” Inji shi.

Da yake jawabi, shugaban kamfanin QAL, Lukman Lawal yace jiragen guda biyu ne wanda kowannensu zai ci mutum 50 ne, kuma za su yi sawu biyar a kowanne rana a kudi mai rangwame, daga Kaduna zuwa Abuja kuma zuwa Legas.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ya kai dansa Abubakar Sadik makarantar gwamnati dake garin Kaduna, Capital School, domin fara karatun firamari a aji daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel