An sace Mai dakin Shugaban Hukumar jiragen kasa a Garin Benin

An sace Mai dakin Shugaban Hukumar jiragen kasa a Garin Benin

Wasu da ake zargin cewa ‘yan bindiga ne sun sace Francisca Okhiria, Mai dakin babban Manajan hukumar NRC na jirgin kasa a Najeriya. Jaridar Daily Trust ta rahoto wannan dazu nan.

Kamar yadda labari ya zo mana a yau 25 ga Satumba, 2019, wadannan ‘yan bindiga sun rika bin dakun Misis Fidet Okhiria ne tun daga filin jirgin saman da ke babban birnin jihar Edo na Benin.

‘Yan bindigan sun yi basaja ne cikin kayan ‘yan sanda wanda ya hana a gane su inda su ka bi ta har kusa da gida, su ka sace ta. A wajen yunkurin sace Okhria ne su ka harbe wani Soji a hanya.

Rahotanni sun bayyana cewa Miyagun sun bindige wannan Soja da ke kan titi ne domin gudun ya kama su. Da aka tuntubi jami’an tsaro, sun tabbatar da aukuwar wannan mummunan labari.

KU KARANTA: Iyalin Sowore sun yi zanga-zanga bayan wata daya da Mai gidan ta

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Edo, DSP Chidi Nwabuzor, ya shaidawa ‘yan jarida cewa an ruga da jami’in sojan da ake harba zuwa wani asibitin Sojoji inda Likitoci ke faman kula da shi

Har ila yau, DSP Chidi Nwabuzor, a madadin ‘yan sandan jihar yake cewa an sace Mai dakin Manajan na NRC ne a daidai gidan Man NNPC da ke karamar hukumar Oredo a cikin jihar ta Edo.

Jami’an ‘yan sanda san tabbatar da cewa an gano motar da Misis Okhiria ta ke ciki lokacin da aka sace ta. Wannan mota babbar samfurin Toyota ce mai bisa kirar Land Cruiser Prado ta zamani.

“Kurtun da ‘yan bindigan su ka harbe Dogari ne da ke tare da ita kuma ‘yan sanda sun kai shi asibitin Sojoji. ‘Yan bindigan sun zo ne a wata mota kirar Toyota Camry, kuma an soma bincike.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel