Yansanda sun kama wasu daliban jami’a 8 dake fashi da makami

Yansanda sun kama wasu daliban jami’a 8 dake fashi da makami

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Neja sun kama wasu daliban jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida dake garin Lapai na jahar Neja su 8 da laifin fashin da makami, inji rahoton jaridae Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daliban sun dade suna fitinar sauran daliban jami’ar ta hanyar kai musu hare haren fashi da makami a dakunansu, kamar yadda Kaakakin Yansandan jahar, DSP Mohammed Abubakar ya bayyana.

KU KARANTA: Izala ta yi Allah wadai da cin fuskar da yan Kwankwasiyya suka yi ma Pantami

Kaakakin yace wasu dalibai ne suka sanar da Yansanda halin da suke ciki na rashin tsaro, inda yan fashi suke bi gidajen dalibai dake wajen makaranta suna musu fashi da kwace, a haka ne wani dalibi ya gane guda daga cikin yan fashin mai suna Yakubu Isah.

“A ranar 22 ga watan Satumba da misalin karfe 6:30 na yamma ne wata daliba mai suna Hauwa Ibrahim tare da wasu mutane 5 suka kai kara ofishin Yansanda inda suka shaida mana cewa da misalin karfe 2:30 na dare yan fashi da makami suka fada cikin gidansu, suka yi musu karkaf tare da raunatasu.” Inji shi.

Yan fashin su ne: Ahmed Kamaldeen, Mohammed Ahmad Hassan, Victor John Dizawo, Abdulrahman Solomon Baje, Hassan Suleiman, Yakubu Isah Kopa, David Solomon da Umar Abdulkareem Sani.

Bugu da kari Yansandan sun ce sun ce sun gano tarin tabar wiwi a dakin Isah a lokacin da suka kama shi, sa’annan yace zasu gurfanar dasu gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike a kansu.

Sai dai da yake zantawa da manema labaru, Yakubu ya musanta aikata fashi da makami, amma yace tabar wiwi nasa ne, kuma ta hanyar cinikin wiwi yake kula da kansa a makaranta. Daga karshe shima rajistran makarantar, Mohammed Abdullahi yace suna hada kai da jami’an tsaro don magance matsalar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel