Sabbin kirkire-kirkire ne hanyar inganta aikin gwamnati, in ji Yemi-Esan

Sabbin kirkire-kirkire ne hanyar inganta aikin gwamnati, in ji Yemi-Esan

- Mukaddashin shugabar ma'aikatan tarayya ta ce kirkire-kirkire ne hanyar inganta aikin gwamnati

- Shugabar ta sanar da hakan ne a taron kwana biyu da ta wata ma'aikatar kimiyya ta Amurka ya shiryawa ma'aikata 80 a Abuja

- Shugaban ma'aikatar ya ce wadanda za a horar din zasu samu gogewar da zasu iya gabatar da aiyuka masu gamsarwa

Mukaddashin shugabar ma'aikatan tarayya, Dr. Folashade Yemi-Esan, ta yi kira akan aikin gwamnati mai inganci.

Ta ce ma'aikatan gwamnati su tashi tsaye don rungumar sabbin kirkire-kirkire don cigaban aikin.

Ta sanar da hakan ne a ranar Talata yayin bude taron kwana biyu na 'radical innovation technology programme' wanda ma'aikatar kimiyya ta Amurka ta shiryawa mutane 80.

Yemi-Esan ta ce akwai bukatar sabbin kirkire-kirkire a fannin aiyukan gwamnati don samun inganci a aikin.

KU KARANTA: 'Yan ta'adda sun mamaye kananan hukumomi 8 a arewacin Borno - 'Dan majalisa

"Yakamata mu kawo sabbin fasahohi na yin abubuwa da dama. Aikin gwamnati ba wai zai ta diban hazaka bane, zai fi kyau idan muna fito da sabbin hanyoyi na kirkire-kirkire," in ji ta.

Daraktan MIT, Dr. Bhaskar Pant, ya ce bashi da tantama cewa wadanda za a horar din zai samar da ilimin zai kara musu kaimi a aiyukansu na fadin kasar.

Ya ce, "Mun san cewa horarwa itace jigo a aikin gwamnati. Ta hakan ne kawai zasu iya gabatar da aiyuka masu gamsarwa ta hanyoyi daban-daban."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.haus

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel