Zan jingine kariyana domin a bincike ni, inji Osinbajo

Zan jingine kariyana domin a bincike ni, inji Osinbajo

Matamakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yace zai jingine kariyar da kundin tsarin mulki ta bashi domin a bincike shi.

“A yan kwanakin da suka gabata, wasu bayanan karya na ta yawo a kafofin watsa labarai akaina, wanda wata kungiyar mahasadda ke ta kitsawa,” ya wallafa a shafin twitter.

“Labarin na bata da suna da batarwar da wannan kungiya ta shirya na ta yawo kafofin sadarwa ba tare da suna ba.

“A yau na bayar da umurnin fara daukar mataki na doka akan wasu mutane biyu, daya Timi Frank da kuma wani Katch Ononuju, wadanda suka sanya sunayensu akan labaran karyan.

“Zan jingine kariyar da kundin tsarin mulku ta bani domin ba kotu damar hukunci akan wannan iikirari na batanci da karya," inji Osinbajo.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Talata a matsayin ranar hutu

Timi Frank, tsohon mataimakin sakataren labaran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yayi zargin cewa hukumar tattara kudaden shiga na tarayya (FIRS) ta bayar da naira biliyan 90 ga mataimakin Shugaban kasa don kamfen din zabe, zargin da tuni hukumar harajin ta karyata.

Amma tuni Frank yayi martani inda ya bukaci hukumar FIRS ta daina yaudarar yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel