Tirkashi: An kama wani mutum yana sayar da tabar wiwi a ofishin NDLEA

Tirkashi: An kama wani mutum yana sayar da tabar wiwi a ofishin NDLEA

Wata babbar kotu dake Legas a ranar Laraba 25 ga watan Satumba, 2019 ta aika da Ayobiojo Hammed gidan yari bisa kama shi da laifin sayar da tabar wiwi a ofishin hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi wato NDLEA na jihar Legas.

Alkalin kotun, Mai-shari’a Sule Hassan ne ya tura da Hammed gidan maza a dalilin laifin da ake tuhumar da aikatawa guda daya kacal na sayar da tabar wiwin da nauyinta ya kai gram 630.

KU KARANTA:An tafka muhawara a Majalisar wakilan Najeriya game da kananan hukumomin da ‘yan Boko Haram suka mamaye

Alkalin ya daga sauraron karar zuwa 11 ga watan Oktoba, 2019 inda za a dawo a cigaba da baje hujjoji dangane da shari’ar.

Lauyan hukumar NDLEA, Fingere Dinneys ya sanar damu cewa an kama Hammed ne tun a ranar 26 ga watan Maris, 2019 a lokacin da yake sayarwa masu aikin gini tabar wiwi a harabar ofishin hukumar dake shiyyar Ikoyi a Legas.

Kotu ta bada tabbacin cewa laifin da ake zargin Hammed da aikatawa ya ci karo da sashe na 20(1)(a) a cikin kundin dokokin NDLEA na shekarar 2004, haka kuma laifin yayi daidai da hukuncin da yazo a sashe na 20(2)(a) cikin dokokin.

Lauyan wanda ake tuhumar, C.W. Ezeonyeziaku bai iya cewa komi ba game da umarnin kotu na ajiye Hammed a gidan yari har zuwa ranar da za a cigaba da shari’ar.

A wani labarin kuwa, zaku ji cewa, Majalisar wakilan Najeriya ta tafka muhawara game da yadda rikici ya ki ci ya ki cinyewa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Bayan tafka wata doguwar muhawara Majalisar ta fitowa gwamnatin tarayya da shawarar kafa gidauniyar hukumomin tsaro, kari a kan kasafin kudin kasa da ake warewa bangaren tsaro.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel