Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Talata a matsayin ranar hutu

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Talata a matsayin ranar hutu

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Talata, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin bikin cika shekaru 59 da samun yancin kai.

Sakatariyar din-din-din na ma’aikatar cikin gida, Misis Georgina Ehuriah, ta sanar da hakan a wani jawabi a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba a Abuja.

Tace ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya kaddamar da hakan a madadin gwamnatin tarayya.

Ministan ya taya yan Najeriya na gida da waje murna a bikin ranar yanci na wannan shekarar.

Ya ba yan Najeriya tabbaci akan jajircewar gwamnati na kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake ciki a kasar.

A cewarsa, zaman lafiya da hadin kai sune matakan cigaban kowace kasa.

Aregbesola yayi kira ga yan Najeriya da su yi koyi ga magabatan kasar kan irin soyayyar da suke wa kasarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel