Babbar magana: Majalisar kasar Iran ta sanya hannu akan wata doka da ta baiwa iyaye maza damar auren 'ya'yansu mata

Babbar magana: Majalisar kasar Iran ta sanya hannu akan wata doka da ta baiwa iyaye maza damar auren 'ya'yansu mata

- Majalisar kasar Iran ta sanya hannu akan wata doka da zata baiwa iyaye maza damar auren 'ya'yansu mata da suka dauka riko

- Wannan doka dai da majalisar kasar ta sanyawa hannu ta jawo kace nace matuka, inda kungiyoyin kare hakkin dan adam suka yo caa akan maganar

- An ruwaito cewa a shekarar 2010 kimanin yara kanana 42,000 'yan shekara 10 zuwa 14 ne suka yi aure

Majalisar kasar Iran ta sanya hannu akan wata doka da zata kare hakkin yara kanana ciki kuwa hadda baiwa wani mutumi damar auren 'yarsa da ya dauko riko duk kuwa da cewa shekarunta 13 a duniya.

Sai dai kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasar sun yo caa akan wannan doka da majalisar kasar ta sanyawa hannu, wacce zata dinga baiwwa iyaye maza damar auren 'ya'yansu mata da suka dauko riko.

Manyan kasar ta Iran, sun duba wannan doka da majalisar ta aika musu sun kuma kwatanta ta da hallacinta a addinin musulunci, amma har yanzu ba ta gabatar da hukunci a kai ba.

KU KARANTA: Tun ina 'yar shekara 12 mijin mahaifiyarmu yake kwanciya dani da kanwata - Wata budurwa ta sanar da kotu

A kasar Iran yarinya 'yar shekara 13 za ta iya aure amma idan alkali ya bayar da dama. Zuwa yanzu dai auren 'ya'yan riko bai hallata ba a kasar.

Yara mata 42,000 ne wadanda suke tsakanin shekara 10 zuwa 14 suka yi aure a shekarar 2010, kamar yadda shafin yanar gizo na Tabnak ya wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel