Habasha: Abiy ya karrama ‘Dan Sandan da ya ki karbar cin hancin N400, 000

Habasha: Abiy ya karrama ‘Dan Sandan da ya ki karbar cin hancin N400, 000

Kishin kasa da gaskiyar wani jami’in ‘Dan sanda a kasar Habasha ta sa Duniya ta yaba da halinsa. Wannan ‘Dan Sanda mai suna Siraj Abdella ya samu jinjina har daga Firayim Ministan kasar.

Kamar yadda mu ka samu labari daga fadar shugaban kasar na Habasha, an yi kokarin ba Siraj Abdella kudin cin hanci domin a shigo da makamai a boye, amma ya ki amincewa da wannan.

Kudin da aka ba wannan jami’in tsaro ya haura N490, 000 wanda a kudin kasar Habasha ya ke kan Birr 40, 000. Wannan abu ya faru ne a Ranar Asabar da ta wuce, 21 ga Watan Satumban 2019.

Wannan namijin kokari da ma’aikacin ya yi wajen hana masu safarar makamai shigowa cikin kasar ya sa Firayim Minista Abiy Ahamed ya gana da shi, ya yabawa kokarinsa da nuna son kasa.

KU KARANTA: 'Yan Kwankwasiyya sun wulakanta Ministan Shugaba Buhari

Firayim Ministan yake cewa Abdella ya sa kasar Habasha a gaban karon kansa inda ya ki karbar rashawar da aka mika masa, ya zabi ya yi aikin da aka ba shi na damke wadannan masu laifi.

A maimakon Siraj Abdella ya karbi tayin da aka yi masa na soke makudan kudi domin ya bada dama a shigo da manyan makamai ta barauniyar hanya, sai ya tsaya kan gaskiya ya damke su.

Abiy Ahmed wanda shi ne Firayim Ministan kasar ya ba wannan Bawan Allah satifiket na girmamawa da jinjina a matsayin ‘dan kishin kasa mai kokarin kare rayukan jama’a a kan dukiya.

A karshen Firayim Ministan na Habasha ya yi kira ga sauran mutanen kasar da sauran jami’an tsaro da su zama masu koyi da hali da dabi’a irin ta wannan Jami’in tsaro mai gaskiya da amana.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel