Buhari ya yi martani kan yunkurin juyin mulki da aka yi a Ghana

Buhari ya yi martani kan yunkurin juyin mulki da aka yi a Ghana

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba 25 ga watan Satumba ya ce ya bi sahun sauran shugabanin kasashen Afrika wurin tir da yunkurin hambarar da gwamnatin jihar Ghana kamar yadda aka ruwaito.

A sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce zamanin yin juyin mulki ko hambarar da gwamnatoci ba tare da zabe ba ya wuce inda kuma ya ce Ghana kasar demokradiyya ta farko a nahiyar.

"Najeriya da Ghana suna kasashe ne da ke tarayya a karkashin ECOWAS kuma alkalluma na Transparency International (IT) da Afrobarometer na 2019 sun nuna cewa kasashen biyu sun samu nasarori sosai a fanin yaki da rashawa.

DUBA WANNAN: 'Yan ta'adda sun mamaye kananan hukumomi 8 a arewacin Borno - 'Dan majalisa

"Duk lokacin da kayi kokarin takawa gurbatattun mutane birki, suma za su yi yunkurin yakar ka. Kamar yadda ake cewa, "Idan kana yaki da rashawa, rashawa shima zai yake ka," inji shugaban kasa

A wurin Buhari, hanya daya tilo na kafa gwamnati a yankin Afirka ta Yamma a wannan karnin na 21 itace ta hanyar zabe na demokradiyya.

A cewarsa, wannan ne hanya kadai na kawo canji a na mulkin kasa.

"Dukkan kasashen Afirka suna girmama Ghana a matsayin ta na kasa ta farko da ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka kuma kasar Afirka ta farko da tayi zabe tsakanin jam'iyyun siyasa. Ghana itace kasar demokradiyya ta farko a Afirka," a cewar Buhari yayin da ya ke nuna goyon bayansa ga gwamnatin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel