Yanzu Yanzu: Sanatoci sun jinjinawa shugaba Buhari akan rufe iyakokin Najeriya

Yanzu Yanzu: Sanatoci sun jinjinawa shugaba Buhari akan rufe iyakokin Najeriya

Biyo bayan rufe iyakar kasar da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi, sanatoci sun yaba ma gagarumin matakin da fadar shugaban kasar Najeriya ta dauka.

An bayyana hakan ne a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, lokacin da Sanata Adamu Aliero ya gabatar da wani jawabi kan muhimmancin rufe iyakar kan tattalin arzikin Najeriya.

Wasu sanatoci biyu sun marawa yunkurin gwamnatin tarayya baya lokacin da suka amince da muhawarar Aliero.

“Na tashi domin marawa wannan lamari baya. Dalili guda da yasa na tashi shine saboda yankina na iyaka da kasar Benin. Ya zama dole mu yaba ma shugaban kasa kan rufe iyakokin domin dakile ayyukan masu fasa kauri.”- Sanata Adeola Solomon.

“Mafita shine tattaunawa da kasashen da ke makwabtaka da mu sannan muyi sintiri a iyakokinmu. A matsayin mu na majalisar dattawa ya kamata mu ba shugaban kasa goyon bayan da yake bukata don kare iyakokinmu.”- Sanata Gabriel Suswam.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram sun kashe wani ma’aikacin agaji da suka yi garkuwa dashi

A halin da ake ciki Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika takardar tsarin kashe kudi da dabarun kasafin kudi na 2020-2022 zuwa ga majalisar dattawa.

Hakan zai bayar da dammar gabatar da kasafin kudin 2020.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya bayar da sanarwar a yayin zaman majalisa a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel