Mutum 3 sun rasa rayukansu a gobarar da ta auku a jihar Kano

Mutum 3 sun rasa rayukansu a gobarar da ta auku a jihar Kano

- Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane uku a gobarar da ta auku a karamar hukumar Ungogo a jihar Kano

- A sa'o'in farko na ranar Laraba ne Malam Mudassir Abdullahi ya kira hukumar don neman tallafin gaggawa

- Mai magana da yawun hukumar ya ce sun hanzarta kai daukin amma sai da aka rasa rayuka uku

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane uku a gobarar da ta cinye wani gida a ranar Laraba da ke Gwayawa Tsohuwa, karamar hukumar Ungogo a jihar Kano.

Mai magana da yawun hukumar, Saidu Mohammed, ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai a Kano ranar Laraba.

Mohammed ya ce wadanda gobarar ta cinye sun hada da yarinya 'yar shekaru biyu kacal a duniya.

KU KARANTA: 'Yan ta'adda sun mamaye kananan hukumomi 8 a arewacin Borno - 'Dan majalisa

"Mun samu kira a sa'o'in farko na ranar Laraba daga wani Malam Mudassir Abdullahi cewa gobara na cin gidansa."

"Bayan samu labarin, mun hanzarta isa gidan don kashe gobarar," in ji shi.

Ya bada sunayen wadanda suka ransu kamar haka: Aminu Bala mai shekaru 50, Rukkaiya Aminu mai shekaru 30, sai Aisha Aminu mai shekaru 2 a duniya.

Mohammed ya ce an mika ragowar gawar wadanda wutar ta ce ga asibitin Murtala Muhammed da ke Kano inda aka tabbatar da mutuwarsu.

Ya ce tuni dai aka fara binciken musabbabin gobarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel