Shugaban majalisar dattawa ya rantsar da kwamiti daban-daban na majalisar

Shugaban majalisar dattawa ya rantsar da kwamiti daban-daban na majalisar

- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan ya rantsar da kwamiti daban-daban na majalisar dattawa

- Ya hori 'yan majalisar da su dubi matsalolin tsaro da rashin aikin yi da ke addabar kasar

- Ya jawo hankali wajen habaka noma da kiwo tare da amfani da albarkatun kasar nan don shawo kan matsalolin

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, a ranar Laraba ya rantsar da kwamiti daban-daban na majalisar.

Yayin rantsarwar, ya hori kwamitin da su tabbatar da sun gabatar da aiyukansu na shawo kan matsalolin kasar nan.

Ya ce, "Kasarmu na fuskantar kalubalen tsaro, matasanmu basu da aiyukan yi da sauran matsaloli. Amma kuma sa'armu daya ita ce muna da isasshiyar kasar noma."

DUBA WANNAN: Kotun zaben ta sauke Mataimakin kakakin majalisar jihar Benue

"Muna kuma da albarkatu da dama a kasar nan. Mai da iskar gas itace jigo a samuwar kudin shigar kasar nan. Kalubalen da muke fuskanta zasu zo karshe idan muka yi amfani da albarkatunmu. Abinda muke bukata kawai shi ne amfani da albarkatun yadda ya dace." In ji shi.

Ya kara da cewa, "Zamu iya shiryawa tare da amfani da noma wajen kawo tsaron abinci har ma da siyarwa kasashen duniya. Hakazalika, albarkatun da ke kasan kasa zamu iya fito dasu ta hanyar da ta dace don amfanarmu."

A don haka ne ya yi kira ga kwamitin mabanbanta da su dubi kalubalen tsaro da rashin aikin yi, tare da gyaran bangarorin man fetur da noma don su zama jagorori wajen aiyukan 'yan majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel