An gina makaranta a kauyen Kano da babu mai wata shaidar kammala karatu

An gina makaranta a kauyen Kano da babu mai wata shaidar kammala karatu

Hukumar Ilimin Kananan Hukumomi (LEA) ta tura hedimasta da malamin makaranta domin kafa makarantar frimari a garin Shara a karamar hukumar Sumaila na jihar Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna kauyen sun dade suna zaune ba tare da makaranta ba hakan yasa mazauna kauyan su kany tafi mai nisa zuwa wasu kauyukan da ke makwabtaka da su domin zuwa makaranta hakan yasa mafi yawancin matasan garin ba su da ko ilimin frimari.

Sanarwar ta jami'in CITAD, Malam Sagiru Ado Abubakar ya fitar ya ce CITAD ta kafa makarantar ne shekaru uku da suka wuce a matsayin gudunmawarta kuma tana kulawa da makarantar.

Ya ce yanzu an yi wa makarantar rajista da hukumar ilimin frimari na sakandare.

DUBA WANNAN: 'Yan ta'adda sun mamaye kananan hukumomi 8 a arewacin Borno - 'Dan majalisa

Abubakar ya kara da cewa wakilan LEA karamar hukumar Sumaila sunyi alkawarin saka makarantar cikin tsarin ta sakamakon malamai biyun da aka aike domin kaddamar da makarantar a hukumance.

Ya ce, "A ranar 10 ga watan Satumban 2019, CITAD ta tafi rabon kayayakin karatu da rubutu da jami'in ilimi na karamar hukumar Sumaila ya hallarta.

"Yayin bikin, jami'in ilimin, Alhaji Sabo Aliyu wanda ya samu wakilcin Malam Uba Mukhtar ya yi alkawarin cewa hukumar Ilimi ta kananan hukumomi za ta samar wa makarantar malami kuma ya bukaci mahukunta makarantar su ziyarci sakataren ilimin domin a musu rajista a hukumance.

"A ranar Talata 17 ga watan Satumban 2019, kwamitin ta ziyarci sakataren ilimin kuma an mata rajista. Yau ina son sanar da ku cewa LGEA ta cika alkawarinta na aiko da malaman makarantu," inji Abubakar.

Ya kara da cewa a ranar 16 ga watan Satumban 2019, al'ummar garin Shara sun tarbi malamai biyu domin kaddamar da makarantar.

Ya kuma roki gwamnatin jihar ta saka garin cikin tsarin ta na bayar da ilimi kyauta don a fara gina ajujuwa inda ya ce garin ta bayar da kyautan fili da za a gina makarantar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel