Sojan Najeriya ya nemi gwamnati ta basu kwalaben giya da buhunan wiwi don yaki da Boko Haram

Sojan Najeriya ya nemi gwamnati ta basu kwalaben giya da buhunan wiwi don yaki da Boko Haram

Rahoton jaridar Information Nigeria ta ruwaito wani jami’in Sojan Najeriya mai suna Emmy Beniso wanda ya roki gwamnati da jama’an Najeriya dasu taimaka ma Sojoji da kwalaben giya da buhunan tabar wiwi domin su ji dadin yaki da yan ta’addan Boko Haram.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Benison ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo daya fitar a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Instagram, inda yace akwai bukatar Sojoji su kasance cikin halin dauke wuta kafin su iya tunkarar mayakan Boko Haram, tare da gamawa dasu.

KU KARANTA: Mabiya darikar Kwankwasiyya sun yi ma Pantami ihun ‘Ba ma yi’, Kwankwaso ya yi shiru

A jawabinsa, Benison yace: “Wani lokaci ba makamai muke bukata ba, abinda muke so kawai shine ku fara tara mana kudade ta yadda zamu sayi buhunan wiwi, katan katan na Alomo, dry gin, Kai Kai, gwamnati ba ta bamu wadannan ba.

“Muna bukatar ya kasance muna matsayi daya na hauka da shegun yan Boko Haram koma fiye dasu idan har muna son gamawa dasu, maganan gaskiya shine kashi 90 na Sojojin Najeriya na zasu iya fuskantar Boko Haram ba tare da sun sha wani abu ba, su ma yan Boko Haram ba haka nan suke ba.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Jami’an hukumar yaki da fasa kauri watau kwastam sun kama wasu dilolin gwanjo guda 235 daga hannun masu fasa kauri a jahar Katsina, wanda hakan ya janyo rikici har mutum daya ya rasu.

Mataimakin kwanturolan kwastam, Bashir Abubakar ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Katsina a ranar Talata, 24 ga watan Satumba, inda yace a ranar Litinin aka kama kayan a garin Jibia.

Ga mai son ganin wannan bidiyo yana iya bin wannan adireshin https://www.instagram.com/p/B2v-qOGH7sj/?utm_source=ig_web_copy_link

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel