Jami’an Yansanda sun kwato tarin bindigu daga hannun dan bindiga a Zamfara

Jami’an Yansanda sun kwato tarin bindigu daga hannun dan bindiga a Zamfara

Jami’an rundunar Yansandan jahar Zamfara sun bankado tarin bindigu guda 30 daga hannun wani gagararren dan bindiga dake jahar Zamfara, mai suna Zakui, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jahar Zamfara, Usman Nagogo ne ya tabbatar da haka yayin da yake bayyana makaman, inda yace sun gano makaman ne a kauyen Lingyado dake cikin karamar hukumar Maru ta jahar.

KU KARANTA: Mabiya darikar Kwankwasiyya sun yi ma Pantami ihun ‘Ba ma yi’, Kwankwaso ya yi shiru

Da yake baje kolin makaman ga manema labaru a babban ofishin Yansandan jahar, Kwamishina Nagogo ya bayyana cewa baya ga wadannan bindigu 30, sun amshi bindigu 49 daga hannun tubabbun yan bindiga, sa’annan yan sa kai sun mika bindigu 200.

Kwamishinan ya kara da cewa an samu wannan nasara ne sakamakon tattaunawar sulhu da gwamnatin jahar Zamfara ta shiga da kungiyoyin yan bindiga da kuma kungiyoyin sa kai domin kawo zaman lafiya a jahar.

“Aikin kwace makamai daga hannun yan bindiga da yan sa kai shi kansa abin alfahari ne, sa’annan ga shi yan bindiga sun sako daruruwan mutanen da suka yi garkuwa dasu, don haka batun amshe makamai ba wai ya tsaya a kan yan bindiga bane kawai, har ma da yan sa kai.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wani gagararren dan bindiga daya shahara wajen satar mutane tare da yin garkuwa dasu a jahar Katsina da Zamfara, Alhaji TK ya gamu da ajalinsa a dalilin barkewar cutar shawara.

Cutar shawara ce ta yi ajalin TK tare da mukarrabansa guda 11, shi dai TK yana da yara yan bindiga sama da 200 da suka mamaye dajin Birnin Gwari, Sabuwa, Faskari, Danmusa, Jibiya har zuwa Nijar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel