Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da 14 a Kaduna

Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da 14 a Kaduna

Wasu yan bindiga wadanda ake zatton masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum daya sannan kuma sun sace akalla mutane 14 a hanyar Birnin Gwari-Kaduna da kauyen Dogon Dawa duk a yankin karamar hukumar Birnin Gwari dake Kaduna.

Lamarin ya auku ne tsakanin ranakun Litinin da Talata.

Daga cikin wadanda aka sace akwai akantan babban asibiti, Jibrin Maigwari da dan majalisar masarautan Birnin Gwari wanda yan bindiga suka sace a hanyarsa ta dawowa daga Kaduna a ranar Litinin.

Wani dan asalin yankin ya bayyana ma majyarmu ta Channels Television cewa yan bindigan har ila yau sun kai farmaki kauyukan Dogon Dawa, a yammacin Talata inda suka buda wuta kan kauyukan, sun kashe mutum daya sannan suka sace mutane shida ciki harda kananan yara biyu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram sun kashe wani ma’aikacin agaji da suka yi garkuwa dashi

Yayin da yake tabbatar da lamarin, kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya bayyana cewa an kubutar da mutane tara daga cikin wadanda lamarin ya cika dasu a ranar Litinin, yayin da ake kokari don ganin an kubutar da sauran mutane hudu.

Duk da haka, ya shawarci mutane da kada su bi hanyar Birnin Gwari idan dare yayi don gudu kada yan bindiga suyi halinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel