A karshe EFCC ta yi magana a kan binciken Osinbajo, shirin N-SIP

A karshe EFCC ta yi magana a kan binciken Osinbajo, shirin N-SIP

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta ce bata binciken mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da shirin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya da aka yi wa lakabi da N-SIP (National Social Investment Programme).

Hukumar EFCC ta ce babu wani wuri ko lokaci da kakakinta, Mista Wilson Uwujaren, ya bayyana cewa suna gudanar da bincike a kan shirin N-SIP ko zargin wadanda ke jagorantar shirin da laifin cin hanci.

EFCC ta ja hankalin jama'a a kan dukkan wasu rahotanni da kan iya lalata alakar mataimakin shugaban kasa da shugaban hukumar EFCC, Mista Ibrahim Magu.

A jawabin da shugaban sashen yada labarai da sadarwa, Mista Wilson Uwujaren, ya fitar, EFCC ta ce Magu na yaba wa shirin N-SIP wajen kokarinsa na tsamo 'yan Najeriya da dama daga cikin kangin talauci.

DUBA WANNAN: Buhari ya kaddamar da lambar ko ta kwana da 'yan Najeriya zasu kira a halin bukatar agajin gagga wa

"Hankalin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya kai kan wani rahoto da ake alakanta wa da shi a kan binciken badakala a shirin N-SIP wanda aka wallafa a wasu kafafen yada labarai ranar Laraba, 25 ga watan Satumba. Wasu kafafen yada labarai sun wallafa rahoton cewa Magu ya ce akwai cin hanci da badakala a cikin shirin N-SIP.

"Rahotannin sun yi ikirarin cewa Magu ya bayyana haka ne ta bakin kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, yayin wani taro da wata kungiya ta gudanar a Kaduna ranar Talata, 24 ga watan Satumba, 2019.

"EFCC na nesanta kanta daga dukkan irin wadannan rahotanni, saboda ba gaskiya bane kuma basu da tushe balle makama," a cewar jawabin.

Hukumar EFCC ta yi kashedi ga kafafen yada labarai a kan yada duk wani rahoto marar tushe da kan iya haddasa rashin jituwa a tsakanin Magu da mataimakin shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel