An tafka muhawara a Majalisar wakilan Najeriya game da kananan hukumomin da ‘yan Boko Haram suka mamaye

An tafka muhawara a Majalisar wakilan Najeriya game da kananan hukumomin da ‘yan Boko Haram suka mamaye

Majalisar wakilan Najeriya ta soma wani yinkurin bude wata gidauniya ta musamman domin tallafa jami’an tsaron Najeriya su kalubalanci matsalolin tsaron dake addabar sassa daban-daban na kasar.

Kamar yadda Majalisar wakilan ta bayyana, abinda aka warewa hukumomin tsaro a cikin kasafin kudin shekara mai zuwa ya yi kadan wurin samar da abinda ake bukata na daga bangaren tsaro.

KU KARANTA:Buhari ya dawo da martabar Najeriya a idon duniya – APC

Wannan muhawarar da aka tafka a Majalisar ta biyo bayan kudurin da, Mohammed Monguno ya gabatar a gaban majalisar ranar Talata 24 ga watan Satumba, wanda ya sanya wa taken ‘Bukatar agajin gaggawa game da yanayin tsaron Najeriya.’

Ilahirin mambobin majalisar sun aminta da wannan kira nasa, inda suka roki gwamnatin tarayya da ta kirkiri gidauniya ta musamman domin tallafawa hukumomin tsaro a matsayin karin a kan kasafin kudin kasa gaba daya.

Haka kuma majalisar ta yi magana a kan muhimmancin sake kulla alaka da sauran kasashen duniya musamman Amurka, domin janye dokar da ta hana Najeriya sayen makaman yaki daga kasashen waje.

Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ya sanar da mu cewa wannan kudurin da Monguno ya gabatar ya zo ne bayan wata ganawar sirri da majalisar ta gudanar da shuwagabannin hukumomin tsaron Najeriya a ranar Litinin.

Gbajabiamila ya ce: “Kamar dai yadda kuka sani a jiya Litinin 23 ga watan Satumba mun yi wata ganawar sirri da shuwagabannin hukumomin tsaron Najeriya na tsawon awa biyar.

“Wannan kuduri na Honourable Monguno yayi daidai da abubuwan da muka tattauna a yayin ganawar. Kuma akwai ganawa ire-iren wadannan dake tafe har zuwa lokacin da majalisarmu ta tabbatar da aiwatar da bukatar ta.”

https://punchng.com/reps-clash-over-boko-haram-takeover-of-borno-lgas/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel