Jonathan ya bukaci naira biliyan 1.2 na sufuri da tsaro in har zai zo min shaida kotu, in ji Metuh

Jonathan ya bukaci naira biliyan 1.2 na sufuri da tsaro in har zai zo min shaida kotu, in ji Metuh

- Tsohon sakataren jam'iyyar PDP, Olisa Metuh ya bukaci babban kotun tarayya da ke Abuja da ta kira Goodluck Jonathan don zamewa shaida garesa

- Ana zargin tsohon sakataren da rub da ciki akan naira miliyan 400 daga cikin kudin makamai

- Amma tsohon sakataren ya ce tsohon shugaban kasar ne ya turo masa kudin don yin wasu aiyukan raya kasa. Don haka kotu ta kirasa don shaida

A ranar Talata 24 ga watan Satumba ne Olisa Metuh, tsohon sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP, ya bukaci babban kotun tarayya da ke Abuja karkashin alkalancin mai shari'a O. E. Abang da ya kira tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan gaban kotun don zama shaida a shari'ar da yake fuskanta.

Metuh da kamfaninsa na Destra Investment na fuskantar shari'a ne da EFCC ta kaisu gaban kotu akan almundahanar kudade har naira miliyan 400.

Ana zarginsa ne da karbar kudin daga ofishin mai bada shawara ta musamman akan tsaro a 2014 ba tare da wani bayani gamsasshe ba.

KU KARANTA: An gurfanar da likitoci biyu a gaban kotu sakamakon ajalin mace mai juna biyu

Metuh ya ce, "Kudin sun shigo ne daga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Ya turo su ne saboda wasu aiyukan raya kasa da za a yi kuma har a waya sai da ya kirani don sanar dani an tura kudin."

"Banyi tsammanin shugaban kasar zai zama jami'in wani mutum ko wani ofishin gwamnati ba, amma nasan yana da mataimaka da yawa da zasu iya yin aiyuka a maimakonsa."

Ya tunatar da kotun cewa, ta kira Jonathan don bada shaida akan ikirarinsa amma kotun bata yi hakan ba.

Ya bayyana cewa lauyan Jonathan na wancan lokacin, Mike Ozekhome ya sanar da shi akwai bukatar ya baiwa Jonathan naira biliyan 1.2 na sufuri da tsaronsa kafin ya iya zuwa bada shaida.

"A yanzu ne na fara jin cewa tsohon shugaban kasar ya musanta sanina kuma baida wata matsala da ni. Ba ni zan kalubalanci rashin zuwansa a matsayin shaida ba. Zan iya tabbatar muku da cewa ya jaddada sai na biyan naira biliyan 1.2," in ji Metuh.

A nan ne EFCC ta gabatar da takardun bukatar da Ozekhome ya gabatar a ranar 27 ga watan Oktoba, 2017 a madadinsa da tsohon shugaban kasar.

Mai shari'a Abang ya dage sauraron karar zuwa ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba, 2019 inda za a kammala cigaba da shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel