Dakarun soji sun kai samame wurin bikin 'yan bindiga da masu garkuwa, sun kama 18

Dakarun soji sun kai samame wurin bikin 'yan bindiga da masu garkuwa, sun kama 18

Rundunar atisayen ofireshon lafiya dole (OPLD) ta tarwatsa wasu gungun matasa da ake zargin mambobin kungiyar matsafa ne da ke aikata miyagun laifuka da suka hada da fashi da makami da garkuwa da mutane a birnin Maiduguri da kewaye.

Dakarun soji sun kai samame wurin da masu laifin ke gudanar da bikin karbar sabbin mambobin da suka shigo cikinsu a ranar Lahadi, 22 ga watan Satumba, 2019.

Mataimakin darektan hulda da jama'a na rundunar OPLD, Kanal Ado Isa, ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

"Mun samu nasarar kama masu laifin ne ta hanyar hada kai da sauran hukumomin tsaro bayan mun samu bayanan sirri a kan al'amurn matasan," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Buhari ya kaddamar da lambar ko ta kwana da 'yan Najeriya zasu kira a halin bukatar agajin gagga wa

"Mun dirar musu a dadida lokacin da masu laifin ke gudanar da bikin karbar wasu sabbin mambobi a cikin kungiyarsu. Sun yi kokarin gudu wa amma basu samu nasara, saboda jami'an tsaron da suka kai samamen suna da yawa," a cewar kanal Isa.

Sannan ya cigaba da cewa "mun kewaye yankin da suke gudanar da taron, kuma mun samu nasarar kama mutane 18 daga cikinsu, wadanda suka hada da daliban jami'ar Maiduguri. Mun kama wasu jami'an rundunar soji uku a tare da su. Mun mika dukkansu ga rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Borno domin zurfafa bincike a kansu."

Kanal Isa ya bayyana cewa tuni rundunar soji ta kori jami'an da aka kama a cikin masu laifin bayan ta gurfanar da su a gaban kotun soji ta musamman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel