Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram sun kashe wani ma’aikacin agaji da suka yi garkuwa dashi

Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram sun kashe wani ma’aikacin agaji da suka yi garkuwa dashi

Rahotanni sun kawo cewa an kashe daga cikin ma’aikata shida na kungiyar da ke yaki da yunwa ta kasa da kasa, wadanda yan ta’addan Boko Haram suka sace watanni biyu da suka gabata.

Yan ta’addan sun wallafa wani faifan bidiyo a yanar gizo, inda suka nuna yadda aka fillewa ma’aikaciyar agajin kai.

Hedkwatar kungiyar ta Action Against Hunger da ke kasar Faransa ta tabbatar da lamarin, jaridar Premium Times ta ruwaito.

A ranar 18 ga watan Satumba, rundunar sojin Najeriya ta tursasa kungiyar da ke yaki da yunwa rufe ayyukanta kan zargin cewa kungiyar mai zaman kanta na taimakawa da rura ayyukan yan Boko Haram.

"#ISWAP sun kashe daya daga ckn ma'akatan agaj shida, wadanda ke aiki tare da kungiyar agaji ta Action Against Hunger da aka yi garkuwa da su watanni biyu da suka gabata a Borno," Mista Salkda ya wallafa a shafinsa na twitter.

"An kashe ma'aikacin agajin ne a wani dan gajeren faifan bidiyo da aka wallafa.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum zai dauki ma'aikata miliyan biyu aiki a Borno

"Kungiyar a cikin bidiyon, tace ta dauki matakin ne akan ma'aikacin saboda" gwamnati ta yaudare su" watanni bayan abunda a yanzu aka sani a matsayin yarjejeniyar sirri tsakanin wata tawaga da ke tsakiya da wasu jami'a da ba a bayyaa ba.

"ISWAP ta kuma yi barazanar kashe sauran ma'aikatan kungyar ma zaman kanta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel