Gwamna Zulum zai dauki ma'aikata miliyan biyu aiki a Borno

Gwamna Zulum zai dauki ma'aikata miliyan biyu aiki a Borno

- Gwamnatin Jihar Borno da kaddamar da shafin intanet da za ta yi amfani wurin daukan ma'aikata miliyan biyu a jihar

- Kwamishinan ma'aikatar kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Babagana Mustapha ne ya kaddamar da shafin

- An kirkiri shafin ne domin tattara bayanai da wadanda za a dauki a aiki a fanin ilimi da sauran kwararru daga mazauna jihar

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kaddamar da shafin intanet da za dauki ma'aikata kimanin miliyan biyu daga sassan daban-daban na jihar aiki.

Kwamishinan ma'aikatan kimiyya da fasaha na jihar, Babagana Mustapha ne ya kaddamar shafin a ranar Talata 2 ga watan Satumban a Maiduguri babban birnin jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mustapha ya yi bayyanin cewa an kirkiri shafin ne saboda tattara bayyanai na wadanda za a dauka aiki na koyarwa da sauran kwararru a jihar a ma'aikatun da ake neman masu aiki.

DUBA WANNAN: Ganduje ya yi wa Saudiyya jinjina ta musamman

A bangarensa, gwamnan ya yi kira ga ma'aikatan tayi hadin gwiwa da ma'aikatar ilimi da sadarwa domin inganta samar da sabis din intanet ga masu neman aiki a jihar.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa gwamnatin Kebbi a ranar Litinin 23 ga watan Satumba ta sanar da fara biyan albashi mafi karanci na N30,000 ga ma'aikatan jihar.

Legit.ng ta gano cewa za a fara biyan sabon albashin a watan Satumban 2019 kamar yadda sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Babale Yauri ya fadi a jawabin da ya yi a Birnin Kebbi.

Ya ce, "Gwamna Atiku Bagudu ya bayar da umurnin fara biyan sabon albashi mafi karanci na N30,000 ga ma'aikatan jihar daga watan Satumban 2019."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel