Kotun zaben ta soke zaben mataimakin kakakin majalisar jihar Benue

Kotun zaben ta soke zaben mataimakin kakakin majalisar jihar Benue

Kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a Makurdi, a jiya Talata ta soke zaben mataimakin kakakin majalisar jihar Benue, Chris Adaji a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Ohimini a jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa kotun ta kuma bayar da umurnin sake yin zabe a mazabun da lamarin ya shafa.

Musa Alechenu Ohimini na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne ya shigar da Ajadi na jam'iyyar PDP kara a kotun zaben kan cewa bai samu adadin kuri'un da doka ta tanadar ba na lashe zabe wanda hakan ya sabawa dokar zabe.

DUBA WANNAN: 'Yan ta'adda sun mamaye kananan hukumomi 8 a arewacin Borno - 'Dan majalisa

A yayin yanke hukuncin, alkalin kotun zaben, Mai shari'a R.O. Odudu ya ce tazarar kuri'un da Adaji ya dara dan takarar APC da shi ba su kai adadin kuri'un da aka soke ba.

A baya, Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewa Adaji ne ya lashe zaben tazarar kuri'u 397 amma kotun zaben ta gano cewa tazarar bai kai 1,065 da aka soke ba a mazabu biyu na Igbanomaje da Odega.

Kotun zaben ta ce bai kamata INEC ta sanar da sakamakon zaben ba ba tare da yin zaben raba gardama ba a rumfunan zaben da abin ya shafa inda ta kara da cewa kamata ya yi hukumar zaben da ce zaben bai kammalu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel