Kotu ta sauke dan majalisar jihar na jam'iyyar SDP, ta maye gurbinsa da dan takarar PDP a jihar Rivers

Kotu ta sauke dan majalisar jihar na jam'iyyar SDP, ta maye gurbinsa da dan takarar PDP a jihar Rivers

- Kotun sauraron kararrakin zabe da ke Fatakwal jihar Rivers ta sauke Dan majalisar jihar karkashin jam'iyyar SDP

- Tuni alkalin ya bukaci INEC da ta mika shaidar komawa majalisa ga Wellington na jam'iyyar PDP don shi ke da kuri'u mafi rinjaye

- Wellington ya garzaya kotun sauraron kararrakin zaben ne tun bayan da aka bayyana Ipalibo George a matsayin wanda ya lashe zaben 9 ga watan Maris

Kotun sauraron kararrakin zabe da ke Fatakwal ta sauke Dan majalisa karkashin jam'iyyar SDP inda ta maye gurbinsa da Dan takarar PDP a majalisar jihar.

Ipalibo George na jam'iyyar SDP da farko shi INEC ta sanar a wanda ya lashe zaben mazabar Asari-Toru na ranar 9 ga watan Maris.

Kotun ta yanke hukuncin Tekenari Wellington na jam'iyyar PDP ne ya lashe zabe kuma ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta mika shaidar komawa majalisar jihar garesa.

Dan takara a karkashin jam'iyyar PDP, Wellington ya garzaya kotun da bukatar a soke nasarar da Dan takarar SDP, George ya yi a zaben 9 ga watan Maris.

KU KARANTA: An dakatar da 'yan majalisar jihar Jigawa biyu na tsawon watanni shida

Mai shari'a J. O. Bangboshe na kotun ya yanke hukuncin cewa Dan takarar PDP ne ke da mafi rinjaye kuma halastattun kuri'un a zaben yankin fiye da Dan takarar SDP din da hukumar zabe ta ce shi ya lashe zaben.

Mai karar ya tabbatar da cewa yawancin sakamakon zaben da aka ba Dan SDP da kuma 'yan sandan duk ba sa hannu, hatimi ko kwanan wata da hukumar INEC ta sanya.

A yayin zantawa da manema labarai bayan kammala shari'ar, Dike Udenna, lauyan wanda ke karar, ya ce kotun ta yanke hukunci ne akan shaidun da aka bayyana gabanta.

"Wanda yayi karar ne ya samu nasara. Tekenari Wellington ne ya lashe zaben da mafi rinjayen kuri'u. Kotun ta umarci INEC da ta mika takardar shaidar komawa majalisa ga Wellington kuma a rantsar da shi bayan gamsuwa da shaidunsa," In ji lauyan.

Hakazalika, lauyan Dan takarar SDP, Immie West, ya ce yana tuntubar saukakken dan majalisar don daukaka kara.

"Muna tattaunawa da wanda nake karewa. Idan nan da kwanaki 21 ba mu daukaka kara ba, toh shi ne fa zai sauka daga kujerarsa. Amma a halin yanzu yana nan a matsayin dan majalisar jihar Rivers," in ji West.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel