Yanzu Yanzu: Buhari ya aika takardar MTEF/FSP na 2020-2022 zuwa majalisar dattawa

Yanzu Yanzu: Buhari ya aika takardar MTEF/FSP na 2020-2022 zuwa majalisar dattawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika takardar tsarin kashe kudi da dabarun kasafin kudi na 2020-2022 zuwa ga majalisar dattawa.

Hakan zai bayar da dammar gabatar da kasafin kudin 2020.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya bayar da sanarwar a yayin zaman majalisa a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba.

Kudin da ake bukatar kashewa na kasafin kudin 2020 ya kasance naira tirliyan 9.97.

Jami’an gwamnatin shugaba Buhari sun yi alkawarin gabatar wa da yan majalisa kasafin kudin 2020 da wuri.

KU KARANTA KUMA: Allah sarki: Yan gida daya su 2 sun rasu cikin sa’o’i 24 a jihar Borno (hotuna)

Shugaban majalisar dattawan ma yayi akawarin aiwatar da kasafin kudin da wurii idan aka gabatar wa da yan majalisar dashi akan lokaci.

A wani lamarin kuma Legit.ng ta rahoto cewa jam’iyya mai mulkin Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta yabawa Shugaba Muhammadu Buhari game da jawabin da yayi a wurin taron Majalisar dinkin duniya karo na 74 a birnin New York.

Mai magana da yawun jam’iyyar APC, Mallam Lanre Issa-Onilu a ranar Talata 24 ga watan Satumba ya ce: “Muna matukar jinjinawa shugaban kasa game da matakin da ya dauka a kan kisan mummuken da ake yiwa ‘yan Najeriya a Afirka ta Kudu, talauci da sauyawar yanayi.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel