Kada ku sassautawa 'yan ta'adda: Sakon shugaban soji ga sojojin Najeriya

Kada ku sassautawa 'yan ta'adda: Sakon shugaban soji ga sojojin Najeriya

- Anyi kira ga dakarun sojojin Najeriya su ragargaji 'yan ta'adda da masu goyon bayansu a yankin arewa maso gabas

- Babban kwamandan Operation Lafiya Dole na sojojin Najeriya, Manjo Janar Olusegun Adeniyi ne ya yi wannan kirar

- Ya ce babu lokacin da ya fi dacewa ga sojojin su kawo karshen 'yan ta'addan na Boko Haram fiye da yanzu

Babban kwamandan Operation Lafiya Dole na sojojin Najeriya, Manjo Janar Olusegun Adeniyi ya yi kira ga sojoji da kada su raga wa 'yan ta'addan Boko Haram da masu goyon bayansu a arewa maso gabashin kasar.

Adeniyi ya yi wannan kirar ne a ranar Talata 24 ga watan Satumba yayin da ya ziyarci hedkwata ta Sector 2 na Operation Lafiya Dole a garin Damaturu babban birnin jihar Yobe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce babu lokacin da ya fi dacewa ga sojojin su kawo karshen 'yan ta'addan na Boko Haram fiye da yanzu.

DUBA WANNAN: An dakatar da 'yan majalisar jihar Jigawa biyu na tsawon watanni shida

"Kada ku raga wa 'yan ta'addan Boko Haram da mutanen da ke goyon bayansu. Dukkan kwamandojin mu za su jagorance ku wurin ragargazan 'yan ta'addan Boko Haram," inji shi.

Ya kuma yi alkawarin bayar da dukkan gudunmawar da ake bukata domin kawar da 'yan ta'addan da su kayi saura a kasar.

A wani rahoton, Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cewa 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP dama suna ficewa daga wuraren da suke buya a yankin Taflkin Chadi suna hijira zuwa yankunan Arewa da Afirka ta Tsakiya.

Mukadashin kakakin rundunar sojin, Kwanel Sagir Musa ne ya sanar da hakan cikin wata jawabi da ya fitar a ranar Alhamis 19 ga watan Satumba a birnin tarayya, Abuja.

Musa ya ce sumamen da Sojojin Najeriya da kuma sojojin hadin gwiwa na kasa da kasa (MNJTF) ke yi wa 'yan ta'addan a wuraren da suka buya ne ya janyo hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel