To fah: Malami ya tilasta dalibansa sun sanya kwalaye a kawunansu saboda kada suyi satar amsa

To fah: Malami ya tilasta dalibansa sun sanya kwalaye a kawunansu saboda kada suyi satar amsa

- Wani Malami mai suna Luis Juarez Texis dan kasar Mexico, ya jawo kace nace bayan wata hanya da ya kawo da zata hana satar amsa

- Malamin ya tilasta dalibanshi sun sanya kwalaye a kawunansu a lokacin da suke rubuta jarrabawa

- Wannan mataki da Malamin ya dauka bai yiwa iyayen yaran dadi ba kwata-kwata, domin kuwa sun nuna fushinsu sosai

Wani Malamin makaranta dan kasar Mexico ya tunzura iyayen dalibanshi bayan wata hanya da ya fito da ita da zata hana dalibai satar amsar jarrabawa a aji.

Kamar yadda aka gani a hoton, Malamin mai suna Luis Juarez Texis wanda ke koyarwa a makarantar Bachilleres El Sabinal, dake Tlaxcala cikin kasar Mexico, ya tilasta daliban shi su sanya kwalaye a kawunansu, wanda zai hana su satar amsar jarrabawa a aji lokacin da suke rubuta jarrabawa.

Wannan labari dai ya jima da yaduwa a kafar sadarwa, bayan iyayen yaran sun nuna bacin ransu akan wannan mataki da Malamin, a takaice ma dai sun nemi makarantar da ta kori Malamin daga makarantar.

KU KARANTA: Wani gari da ake biyan zauna gari banza naira dubu talatin (N30,000) a kowacce rana su dinga kwashe shara

Iyayen yaran sun wallafa sako a kafar sadarwa akan irin yadda Malamin ya ci zarafin 'ya'yansu a cikin aji.

Sannan suka nemi gwamnati ta dauki mataki domin kare hakkin yaransu, sannan suka nemi a kori Malamin daga makarantar, inda suka bayyana abinda yayi a matsayin abinda bai dace ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel