Buhari ya dawo da maratabar Najeriya a idon duniya – APC

Buhari ya dawo da maratabar Najeriya a idon duniya – APC

Jam’iyya mai mulkin Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta yabawa Shugaba Muhammadu Buhari game da jawabin da yayi a wurin taron Majalisar dinkin duniya karo na 74 a birnin New York.

Mai magana da yawun jam’iyyar APC, Mallam Lanre Issa-Onilu a ranar Talata 24 ga watan Satumba ya ce: “Muna matukar jinjinawa shugaban kasa game da matakin da ya dauka a kan kisan mummuken da ake yiwa ‘yan Najeriya a Afirka ta Kudu, talauci da sauyawar yanayi.”

KU KARANTA:Bincike: Wamakko ya ce a shirye yake da ya bayyana gaban hukumar EFCC

Jam’iyyar ta kara da cewa: “Duba ga irin yadda kimar Najeriya take rawa a idanun kasashen duniya, da zuwan wannan gwamnatin ta Shugaba Buhari yanzu za ka iya fadi kanka tsaye cewa martabar Najeriya a idon duniya ya dawo.”

Taken zaman Majalisar na bana shi ne ‘Hadin gwiwar kasa da kasa domin kawar da talauci, samar da ilimi mai inganci da kuma lura da sauyawar yanayi. Akwai bukatar a samu Najeriya mikakkiya domin cinma wadannan abubuwa da aka ambata.

“A yayin da gwamnati ke kokarin kawar da talauci ta hanyar bunkasa tattalin arziki, akwai shirye-shirye na musamman da aka fitar domin samarwa matasa ayyukan yi. Har wa yau, gwamnati na cigaba da yaki da ta’addaci da kuma matsalolin tsaro.

“Shirye-shiryen rage zaman banza da ke cigaba da gudana a Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen rage talauci a tsakanin dai-daikun mutanen Najeriya.

“Haka kuma a cigaba da yunkurin gwamnati na habbaka tattalin arziki, an samarwa mata da matasa hanyoyin aikin a bangaren noma da kuma hakar ma’adanan kasa. Duk da cewa bamu gama ayyukan da muka fara ba, amma idan kuka yi waiwaye zaku ga inda muka baro da inda muke a yanzu sun bambanta.” Inji jam’iyyar APC.

https://www.vanguardngr.com/2019/09/unga-buharis-address-has-restored-nigeria-to-respectable-intl-standing-%E2%80%95-apc/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel