Damfara: Ta yi yunkurin batawa wani Dan majalisar wakilai suna, ta karba makuden kudade daga wurinsa

Damfara: Ta yi yunkurin batawa wani Dan majalisar wakilai suna, ta karba makuden kudade daga wurinsa

- Wata mata mai suna Nkeiruka Cynthia Kamalu ta yi yunkurin batawa Dan majalisar wakilai suna a jihar Imo

- Ta zargesa da yi mata fyade tare da dirka mata ciki wanda ta hakan ta dinga karbar manyan kudade a hannunsa

- Tuni dai jami'an 'yan sanda suka cafketa tare da wadanda suka hada kai wajen damfarar

Hukumar 'yan sandan jihar Imo sun cafke wata mata mai suna Nkeiruka Cynthia Kamalu da laifin damfara tare da yunkurin bata sunan wani dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabarA Ohaji/Egbema/Oguta/Oru na jihar Imo.

Nkeiruka ta yi ikirarin cewa Dan majalisar yayi mata fyade inda har ta samu juna biyu.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar, SP Orlando Ikeokwu, ya yi bayani game da hakan a Owerri babban birnin jihar.

Ya ce, a ranar 5 ga watan Mayu, an kawo mana karar Kamalu akan damfara, hadin kai wajen cuta da kuma barazana ga rayuwa.

Kamalu ta yi ikirarin cewa tana dauke da jikin Dan majalisar tare da barazana wacce ta sa ya dinga tura mata makuden kudade har da kudin tafiya Canada inda zata haifa cikin da take dauke dashi.

KU KARANTA: An gurfanar da likitoci biyu a gaban kotu sakamakon ajalin mace mai juna biyu

Daga baya ta ce masa, ta haifi 'yan biyu inda ta ce daya ya rasu kuma ta turowa Uju hoton jariri daya.

Ikeokwu ya ce ingantaccen bincike ya nuna cewa Kamalu bata dau ciki ba amma ta hada baki ne da wani Emeka Muoneke don sayen jinjiri a naira miliyan 1.8.

'Yan sandan sun gano cewa Kamalu bata je Canada ba, kawai ta samu wani tsari ne da ke nunawa Dan majalisar lambar kasar waje idan ta kirasa.

Ikeokwu ya ce, Kamalu da Muoneke sun amsa laifukansu kuma sun jagoranci 'yan sanda zuwa Nnewi inda ta sayi jinjijirin. Tuni dai 'yan sanda suka cafke duk wadanda ake zargin wanda ya hada da wani likita kuma an mikasu kotu.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce sun mallaki bayanan kiran waya da sakonnin karta kwana da Kamalu ta dinga turawa Dan majalisar.

Ikeokwu ya kara da cewa, ikirarinta na fyadenmu duk na bogi ne kuma ta yi ne damfara da wasa da hankalin jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel