‘Ya ‘yan mu su na kewar Mahaifinsu – Matar Sowore ta ja zuga zuwa UN

‘Ya ‘yan mu su na kewar Mahaifinsu – Matar Sowore ta ja zuga zuwa UN

Uwargidar Omoyele Sowore, mai gidan jaridar nan ta Sahara Reporters wanda aka garkame a Najeriya bayan kawo zanga-zangar juyin-juya mai taken #RevolutionNow, ta fito ta na kokawa.

Kamar yadda mu ka samu labari daga gidan Talabijin na CNN a jiya Talata, Mai dakin Omoyele Sowore ta jagoranci wata zanga-zanga da aka shirya a Hedikwatar majalisar dinkin Duniya.

An yi wannan zanga-zanga ne a lokacin Muhammadu Buhari ya ke jawabi a zauren majalisar gaban sauran shugabannin Duniya. Opeyemi Sowore ta yi kira ga Buhari ya saki Mai gidan na ta.

Wannan Baiwar Allah ta koka da cewa an hana Mijin na ta ganawa da ‘yanuwansa tun bayan da aka kama shi aka tsare yau fiye da wata guda kenan, sau biyu ta iya magana da shi ta waya.

KU KARANTA: Jawabin Shugaban kasa Buhari a gaban Majalisar Dinkin Duniya

Opeyemi ta ke cewa: “Abin takaici ne ace wannan lamari ya kai wata daya da rabi, musamman ace ga wanda yake kiran ganin an canza Najeriya.” Haka zalika Matar ta kuma kara da cewa:

Yara su na da juriya, amma yanzu su na kewan Mahaifinsu. Kuma su na fatan dawowarsa cikin koshin lafiya.” Matar sabon shiga siyasar ta ce watanni kusan biyu kenan rabon da su gan shi.

Tun sa’ilin da jami’an DSS masu fararen kaya su ka yi gaba da ‘dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar AAC a zaben 2019, har Mai dakinsa sau biyu rak ta iya jin muryarsa ta wayar salula.

Yanzu gwamnatin kasar sun maka shi a kotu bisa zargin aikata wasu manyan laifuffuka. Bayan nan ne kuma aka ji cewa babban kotun tarayya da ke Abuja ta nemi DSS ta yi maza ta sake shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel