Tirkashi: Sabon rikici ya kunno kai gadan-gadan a APC

Tirkashi: Sabon rikici ya kunno kai gadan-gadan a APC

Wutar rikici na ruruwa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki yayinda shugabannin jam’iyyyar na jihohi 36 da babban birnin tarayya suka tashi daga wata ganawar gaggawa, a Abuja, inda suka yi Allah wadai da abunda suka bayyana a matsayin rashin karrawar da ya dace a jam’iyyar.

Sun yi korafin cewa hatta ga wadanda suka kafa jam’iyyar da wadanda suka sha wahala wajen ganin nasarar jam’yyar a matakai daban-daban duk yasar dasu yayinda wasu da suka zo daga sama ke cin moriyar abunda basu shuka ba.

A wani jawabi da aka gabatar bayan taron, shugabannin sunce an doshi magoya bayan APC a fadin kasar da abun kunya da tozarci a matakai daban-daban; inda suka bayyana cewa anyi wats da tsarin jam’iyyar baki daya.

Jawabin na dauke da sa hannun shugaba da kuma sakataren kungiyar, Ali Bukar Bolari da Ben Nwoye. Su duka byyun sun kasance shugabann jam’iyyar a jihohin Borno da Enugu.

KU KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara ta jingine hukunci akan karar da Dino Melaye ya shigar

Daga cikin gibin, sun bayyana cewa anyi watsi da shugabannin wadanda ke jan ragamar jam’yyar a jihohinsu kwata-kwata ta bangaren nade-naden mukaman tarayya.

Abu mafi munni, kungiyar ta koka akan gudanarwar harkokin jam’iyyar ba tare da sakataren kasa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel