'Yan ta'adda sun mamaye kananan hukumomi 8 a arewacin Borno - 'Dan majalisa

'Yan ta'adda sun mamaye kananan hukumomi 8 a arewacin Borno - 'Dan majalisa

Ahmadu Jaha, dan majalisar wakilai na tarayya daga jihar Borno ya ce 'yan ta'adda sun mamaye kananan hukumomi takwas cikin 10 da ke arewacin jihar.

Dan majalisar wanda dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne da ke wakiltan mazabun Damboa/Gwoza/Chibok a majalisar ya fadi hakan ne yayin zaman majalisar a ranar Talata kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A yayin jawabinsa kan kudirin neman ware kudi na musamman ga jami'an tsaro domin yaki da 'yan ta'adda, ya ce akwai abubuwan da ake yi a boye game da yaki da 'yan ta'adda.

A yayin da ya ke kokawa kan karuwar ta'addanci a yankin arewa maso gabas, dan majalisar ya ce 'yan ta'addan suna kai hare-hare wasu bangarorin jihar Borno a baya-bayan nan.

DUBA WANNAN: An dakatar da 'yan majalisar jihar Jigawa biyu na tsawon watanni shida

Ya ce, "Akwai garuruwa da dama a Borno da wasu jihohin da ke fama da matsalar 'yan ta'adda da ke karkashin 'yan ta'addan.

"Misali, a karamar hukumar da ke da mazabu 13 kamar nawa wato Gwoza, kimanin uku zuwa hudu ne ba karkashin 'yan ta'adda su ke ba.

"A Chibok, akwai mazabu 10, biyu ne kadai ba su karkashin Boko Haram. A Damboa, akwai mazabu 10, daya ne kawai baya karkashin Boko Haram. Wannan kawai yankin Chibok/Damboa/Gwoza kenan.

"Bulaliyar majalisa zai iya min shaida, cikin kananan hukumomi 10 da ke arewacin Borno, guda biyu ne kawai ba karkashin 'yan ta'adda su ke ba."

Kawo yanzu, Kakakin rundunar soji, Sagir Musa bai mayar da martani kan kalaman da dan majalisar ya furta ba kan ikirarin da gwamnati da rundunar soji tayi na cewa ta ci galaba kan 'yan ta'adda kuma ba su rike da wani gari a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel