Kotun daukaka kara ta jingine hukunci akan karar da Dino Melaye ya shigar

Kotun daukaka kara ta jingine hukunci akan karar da Dino Melaye ya shigar

Kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar Talata, 24 ga watan Satumba, ta jingine hukunci a kararraki uku da sanata mai wakiltan Kogi ta Kudu, Dino Melaye, ya shigar inda yake kalubalantar nasarar zabensa da kotun sauraron kararrakin zaben majalsar dokoki ta soke.

PDP da Melaye sun daukaka kara uku nda suke rok kotun da ta jingine mafi akasarin hukuncin kotun zaben wacce ta soke zaben Melaye a matsayin Sanata mai wakltan Kogi ta tsakiya.

Justis Abubakar Datti Yahaya wanda ya jagoranci sauraron kararrakin uku ya sanadar da cewar za a sanar da ranar yanke hukunci ga bangarorin da abun ya shafa da zaran sun sanya rana.

PDP, wacce ta samu wakilcin Jubrin Okutepa (SAN), a muhawararsa na karshe ya roki kotun daukaka karar da ta jingine mafi akasarin hukuncin kotun zaben akan Mista Melaye kan hujjar rashin bayar da hurumin jin ta bakinsa da kuma kin duba hujjar da aka gabatar lokacin sauraron karar.

Jam’iyyar tayi ikirarin cewa kotun zaben ta gaza duba bayanan shaidunta yayinda babu wani nuni da aka yi ga dukkan takardun da suka gabatar a matsayin hujja kafin kotun zaben ta yanke hukunci mai cike da kuskure kan zabe.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyyar APC ta daukaka kara zuwa kotun koli a kan PDP da Atiku

PDP ta cigaba da ikirarin cewa kotun zaben ta juya tsarin adalci lokacin da ta yi amfani da zarcewar kuri’u wajen soke zaben sanatan kan adadin katin zaben da aka karba maimakon masu zabe da aka yiwa rijista kamar yadda doka ta tanadar.

Don haka PDP ta bukaci kwamitin mutum uku na kotun da su yi amfani da sashi na 16 da dokar kotun daukaka kara sannan ta soke lamarin akan rashin inganci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel