Bincike: Wamakko ya ce a shirye yake da ya bayyana gaban hukumar EFCC

Bincike: Wamakko ya ce a shirye yake da ya bayyana gaban hukumar EFCC

A yayin da maganganu ke cigaba da yawo a kafafen yada labarai game da tuhumar da hukumar yaki da cin-hanci take yiwa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko mai wakiltar Sokoto ta tsakiya, a ranar Talata 24 ga watan Satumba ya ce zai gabatar da kansa ga hukumar.

Wannan labarin ya fito daga wani zancen da mai magana da yawun bakin sanatan, Bashir Rabe Mani ya fitar.

KU KARANTA:Majalisar dattawa na neman Aregbesola da Dingyadi game da Kwalejin ‘Yan sanda

Inda ya ke cewa, labarin da ke yawo a kafafen sadarwa na ambatar sunayen Sanata Wamakko da Kwankwanso inda ake cewa sun yi sama da kudin da ya haura biliyan N18 a lokacin da suke gwamnoni.

Wamakko ya ce an fitar da wannan maganar ne domin kawai a bata masa suna, inda ma har ya kalubalanci masu zargin da su wallafa bayanan asusun ajiyarsa na banki.

“Ba wannan bane lokaci na farko da aka soma yi man irin wannan abin, karo na farko shi ne a watan Afrilun 2018. Amma sai dai hakarsu ba ta cinma ruwa ba a wancan lokacin, warwas suka fadi saboda abinda suka so bai samu ba.” Inji Wamakko.

Haka zalika, Sanata Wamakko ya karyata batun cewa hukumar EFCC ta turo masa da sammaci. A cewarsa, “Karyane hukumar EFCC ba ta bani goron gayyata ba, masu son bata min sunane ke yada wannan labari.”

A karshe Sanatan ya bayyana kansa a matsayin dan-adam wanda bai wuce aikata kuskure ba, kuma ya kara da cewa a shirye yake da ya bayyana a gaban hukumar idan har an bukaci yayi hakan, amma ba wai shaci fadin kafofin sadarwa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel