'Yan sanda sunyi martani kan rahoton sace matafiya 13 a titin Kaduna zuwa Abuja

'Yan sanda sunyi martani kan rahoton sace matafiya 13 a titin Kaduna zuwa Abuja

Gwamnatin Jihar Kaduna ta karyata labarin da aka wallafa a wasu kafafen yada labarai na cewa masu garkuwa da mutane sun sace mutane 13 a babban titin Kaduna zuwa Abuja.

Ta ce labarin ba gaskiya bane kuma wadanda suka kirkiri labarin sunyi hakan ne domin razana matafiya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa wasu mutane sanye da kayan sojoji sun yi kutse cikin gidajen wasu mutane a kusa da kauyen Dutse da ke karamar hukumar Chikun na jihar a ranar 23 ga watan Satumban 2019 misalin karfe 1.30 inda suka sace mutane shida su kayi awon gaba da su.

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo ya tabbatar cewa daya daga cikin wadanda aka sace mai suna Umar Abbas mai shekaru 32 ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen ya kuma kai rahoto wurin 'yan sanda.

DUBA WANNAN: An dakatar da 'yan majalisar jihar Jigawa biyu na tsawon watanni shida

A cewar sanarwar: "Rundunar 'yan sandan tana son fayyace cewa lamarin bai faru da matafiya a titin Kaduna zuwa Abuja ba kuma adadin mutanen da aka fadi a rahoton ba gaskiya bane.

"Kwamishinan 'yan sanda CP Ali Janga ya aike da jami'ansa nan take domin zuwa wurin da abin ya faru da niyyar ceto wadanda aka sace da kama wadanda suka aikata mummunar aikin.

"Kwamishinan 'yan sandan ya damu kan yadda aka sace mutane yayin da suke harkokinsu. Sai dai wannan ba dama bace na yin karya kan abinda ya faru da canja adadin mutanen da abin ya shafa don tsorata matafiya."

Ya yi kira ga al'ummar jihar Kaduna su cigaba da bawa rundunar hadin kai ta hanyar taimakawa rundunar da bayyanai masu amfani cikin gaggawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel