Tirkashi: Likita ya cirewa majinyaci lafiyayyun kodojinsa biyu

Tirkashi: Likita ya cirewa majinyaci lafiyayyun kodojinsa biyu

- An gurfanar da Dr Yakubu da laifin cirewa majinyaci kodojinsa lafiyayyu duk biyun wanda hakan yayi sanadin rayuwarsa

- Marar lafiyan ya tunkari likitan ne da korafin ciwon ciki a wani asibiti da ke Jimeta

- Bayan kwanaki uku da yi masa aikin 'yan uwansa suka komawa likitan sakamakon rashin matsalar rashin yin fitsari da ta bullo

Kotun kungiyar likitocin Najeriya ta gurfanar da Dr Yakubu Hassan Koji da laifin cirewa Isa Hamma kodojinsa wanda ya yi sanadiyyar rasa ransa.

Likitan ya farka majinyacin ba tare da sanar da shi kalubalen da zai iya fuskanta ba a gaba.

Isa Hamma ya tinkari likitan da korafin cewa yana fama da ciwon ciki. A ranar 8 ga watan Yuli, 2016, likitan ya yi wa Hamma aiki har ya cire masa kodojinsa.

Bayan kwanaki uku da faruwar hakan ne aka gano cewa Hamma baya iya fitsari. Ciwo ya cigaba inda har ya fara kumburi a fuska da hannayensa wanda hakan yasa 'yan uwansa komawa ga likitan da aka zargi.

Daga baya dai likitan ya turasu asibitin tarayya da ke Gombe. A nan ne likitoci dai suka tabbatarwa da 'yan uwan Hamma cewa ba shi da koda. Daga baya dai Hamma ya ce ga garinku. Hakan ne kuwa yasa 'yan uwansa suka maka likitan a kotu.

KU KARANTA: An gurfanar da likitoci biyu a gaban kotu sakamakon ajalin mace mai juna biyu

Da farkon gurfanar da likitan da aka yi gaban kotun kungiyar likitocin, an tuhumesa da laifuka 12 inda ya amsa 2 daga ciki. Kafin tashi zaman kotun, sai aka ba wa Yakubu shawarar kawo lauyan don cigaba da shari'ar.

A jiya Talata, 14 ga watan Satumba, kotun ta dawo sauraron shari'ar inda Yakubu ya kawo lauyansa. Bayan kara maimaita masa zargin da ake masa, sai ya musanta tare da cewa shi bai aikata ba.

Shugaban kotun, Farfesa Abba Hassan ya sanar da duk wanda yake kotun cewa da farko Dr Yakubu ya amsa laifinsa amma sai ya roki kotun inda ta aminta da ya samo lauya.

"Matsalar itace cire kodojin majinyacin bayan lafiyayyu ne kuma suna aiki. Hakan kuwa shi ya yi sanadin rasa ran majinyacin. Koda zaka roki kotu rangwame, abu mafi mahimmanci shine ba dokarmu kadai ka take ba."

A yau Laraba kotu zata cigaba da sauraron karar inda zata yanke masa hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel