Saraki: Na bada cikakken rahoton yadda na kashe kudin Majalisar Tarayya

Saraki: Na bada cikakken rahoton yadda na kashe kudin Majalisar Tarayya

Tsohon shugaban majalisar dattawam Najeriya, Bukola Saraki, ya tofa albarkacin bakinsa a kan jita-jitar da ke yawo na cewa shi da mataimakinsa, sun ki bada bayani a kan wasu makudan kudi.

Bukola Saraki ya yi watsi da rahotannin cewa shi da Sanata Ike Ekweremadu da ya rike kujerar mataimakin shugaban majalisa a lokacinsa, ba su bayyana inda su ka kai kudin da aka ba su ba.

Dr. Saraki ya karyata wannan zargi ne ta bakin babban Hadiminsa na yada labarai, Yusuph Olaniyonu. Olaniyonu yace Mai gidan na sa ya bada diddikin duk abin da ya faru kafin ya bar ofis.

Olaniyonu yace: “Saraki ya fitar da bayani kan duk wani kudi da aka warewa ofishinsa domin harkokin gudanarwa a lokacin da yake shugaban majalisa tsakanin Yunin 2015 zuwa Mayun 2019.

Mista Yusuph Olaniyonu ya bada karin bayani da cewa kafin Bukola Saraki ya bar kujerar majalisar tarayya a Ranar 6 ga Watan Yunin 2019, sai da ya fadi inda duk ya kashe kudin ofishin.

KU KARANTA: FIRS ta karyata zargin ba APC makudan kudi domin ta yi kamfe

“An ba Bukola Saraki satifiket na Certificate of Retirement mai nuna shaidar cewa ya bi dokoki da ka’idojin da su ka shafi bada rahoto kan yadda aka batar da duk wani kudi a lokacinsa. Inji Yusuf Olaniyonu.

A baya wata jarida ta rahoto cewa Sanatoci Bukola Saraki da Ike Ekweremadu sun bar ofis ne a tsakiyar bana ba tare da sun yi bayanin abin da su ka yi da kudin da aka rika ware masu a shekaru hudu ba.

Abubukar Bukola Saraki ya rike kujerar shugaban majalisar dattawa kuma shugaban ‘yan majalisar tarayya ne na shekaru hudu. Wa’adinsa ya zo da rikicin siyasa da binciken hukuma daban-daban.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel