Jam'iyyar APC ta daukaka kara zuwa kotun koli a kan PDP da Atiku

Jam'iyyar APC ta daukaka kara zuwa kotun koli a kan PDP da Atiku

- Jam'iyyar APC ta daukaka kara itama a kotun koli akan shari'ar da ta gabata

- APC na da bukatar kotun kolin ta kara duba wasu sassa na shari'ar da kotun daukaka kara ta yi

- Daga cikin shaidun da jam'iyyar ke bukatar kotun ta kara dubawa su ne shaidu masu lamba 40, 59 da 60

Jam'iyyar APC ta daukaka kara mai kalubalantar sashin hukuncin zaman kotu da aka yi a ranar 11 ga watan Satumba.

Karar na bukatar soke shaidun da PDP ta gabatar wadanda kotun sauraron kararrakin zabe ta aminta dasu.

A daukaka karar da APC tayi a ranar Talata, APC ta bukaci kotun kolin da ta soke wasu shaidu da ta aminta dasu a kotun daukaka kara ta Najeriya.

Bayan yanke hukuncin a ranar 11 ga watan Satumba wanda ya tabbatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kujerarsa, a ranar Talata PDP ta shigar da kara gaban kotun koli akan kalubalantar shari'ar.

PDP da Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar, Atiku Abubakar, ya ce kotun daukaka kara da ta saurari shari'arsu ta yi kuskure da ta ce babu bukatar Buhari ya miko takardun shaidar makarantarsa.

KU KARANTA: An gurfanar da likitoci biyu a gaban kotu sakamakon ajalin mace mai juna biyu

PDP ta kara da cewa, kotun sauraron kararrakin zaben ta yi kuskure da ta yanke hukunci bayan kuwa shugaban kasa Buhari bai kawo shaidu isassu na ikirarin da yayi cewa ya yi makarantar sakandire ba.

Amma kuma a karar da APC ta shigar a ranar Talata, ta bukaci kotun kolin da ta kara duban hukuncin kolin na karbar shaida mai lamba 40, 59 da 60.

Shaidun da bayyanarsu ke zama kalubale ga APC sune, Segun Showunmi, mai magana da yawun Atiku wanda ya bayyana gaban kotun tare da mika wani faifan bidiyo da ya kunshi zancen jami'in INEC a jihar Bayelsa, Mike Igini, wanda ya ce INEC na da shirin tura sakamakon zabe ta 'server'.

Sauran shaidun biyu masu lamba 59 da 60 su ne: David Njorga da Joseph Gbenga.

APC na bukatar kotun ta cire akalla sakin layi 43 daga cikin takardun PDP.

Lauyan APC, Lateef Fagbemi ne ya mika bukatar jam'iyyar ga kotun kolin.

Har yanzu dai kotun kolin bata sa ranar jin kararrakin da aka daukaka ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel