Mata ta ci kafar kare ganin Abokin kwanciyarta ya mutu daga ita sai shi

Mata ta ci kafar kare ganin Abokin kwanciyarta ya mutu daga ita sai shi

Wata Baiwar Allah da har yanzu ba gane ta ba, ta tsere daga gari a dalilin mutuwar wani Dattijon Masoyinta. Da alamu Raji Adio ya mutu ne a lokacin da su ke tarawa a cikin daki a wani otel.

Kamar yadda mu ka samu labari, wannan abu ya faru ne a otel dinnan na River Bank wanda ke cikin Unguwar Ijora-Badia a Garin Legas. Yanzu dai ana neman wannan mata an rasa inda ta yi.

Bayan Marigayin ya biya kudi ya kama kudin daki ne Manajan wannan otel mai suna Williams Ekezie, ya ba shi mabudi. A nan ne ya nufi daki da wata Mata, su ka shiga zabga soyayyarsu.

Mai otel din ya fita da safe domin ya yi ibada a wani coci da ke kusa da wannan otel kenan sai ya ga wannan Mata da aka shiga daki da ita ta fito a guje ta tsere kafin kowa ya iya cin mata.

Ma’aikatan otel din sun bayyanawa ‘yan jarida cewa Dattijon ya saba kawo wannan mata daki. Sai dai a lokacin da aka samu wannan bacin rana, ma’aikatan duk sun tafi coci da safe domin ibada.

KU KARANTA: Saura kiris wata Mata ta kashe Surukarta a Jihar Kano

Wani Mai shara a wannan otel din, John Chuks, shi ne ya ga Matar a lokacin da ta ke fitowa za ta tsere a guje. A maimakon ya bi sawunta, sai ya yi yunkurin zuwa coci domin ya sanar da mu.”

Manajan otel din ya kara da cewa: “Lokacin da mu ka koma dakin don mu ga abin da ya faru, sai mu ka ga Adio a kwance tsirara, mu na bincikawa sai mu ka fahimci cewa ya ce ga garin ku nan.”

“Mun kuma samu tsumma a kasar dakin, sannan duk tufafinsa su na kwance a kasa. Ina zargin Matar ta tashi ta sanya kayanta ne, ta tsere bayan Mista Adio ya rasu.” Inji Manajan wannan otel.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Legas, Bala Elkana, ya tabbatar da cewa ana binciken abin da ya faru domin tabbatar da abin da ya kashe Adio. A dalilin haka ne aka tsare Chuks na wani ‘dan lokaci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel