Obasanjo ya sa aka sauke ni daga kujerar Gwamna a 2006 - Rashidi Ladoja

Obasanjo ya sa aka sauke ni daga kujerar Gwamna a 2006 - Rashidi Ladoja

Tsohon gwamna Rashidi Ladoja, ya bayyana cewa rashin goyon bayan Olusegun Obasanjo ya kara wa’adi na uku a ofis ta sa aka tsige sa daga mulki. Ladoja ya yi wannan bayani ne kwanan nan.

Rashidi Ladoja wanda ya taba barin mulki a 2006 yake cewa tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi kutun-kutun din sauke sa ne saboda bai goyi bayan ya cigaba da zarcewa a kan mulki ba.

Tsohon gwamnan ya ce an yi kokarin shawo kan Obasanjo da sa bakin irinsu Emmanuel Alayande da tsohon Minista Prince Bola Ajibola, domin ya hakura da batun sauke shi amma ya ki.

Ladoja wanda ya koma mulki a karshen 2016 ya ke cewa Obasanjo ne ya yi ruwa ya yi tsaki wajen ganin ya bar gidan gwamnatin jihar Oyo ba Marigayi Adedibu kamar yadda wasu ke tunani ba.

Tsohon gwamnan yake cewa: “Ni ma na yi kuskure daya. A lokacin da na samu labarin Obasanjo ya na so ya sake zarcewa a ofis, sai na tambayesa ko da gaske ne, ya ce sam, sai na ce Madalla.”

Kuru-kuru ya ce masa: “Baba (Obasanjo), ba don haka ba, da na ce da kai ba ka san Ubangiji ba, Ubangiji ne ya sa ka yi mulki na shekara takwas ba don ka cancanci ka yi mulkin kasar nan ba.”

KU KARANTA: Gwamnoni sun roki Gwamna Wike ya sasanta da Shugaban Jam’iyya

Rashidi Ladoja ya cigaba da cewa: “Obasanjo kuwa ya hakikance a kan ya cancanci mulki, sai na fada masa a mulkin farar hula, ‘yan siyasa su na tsayawa takara ne, kai kuwa dauko ka aka yi.”

Gwamnan yake cewa bayan ya koma gida ne Takwaransa na jihar Ogun, Gbenga Daniel, ya kira sa inda ya fada masa Obasanjo ya yi alkawarin sai ya ga bayansa don haka ya je ya ba shi hakuri.

Daga nan ne Ladoja ya yi kokarin zuwa taro domin ya shawo kan Obasanjo inda ya iske shi tare da babban jigon jam’iyyar PDP a lokacin, Oyewole Fasawe. A karshe ba su iya yin magana ba.

A karshe dai aka dauki gwamnoni irinsu Soye Oyinlola, Olagunsoye Oyinlola, Gbenga Daniel domin a ba Obasanjo hakuri, inda shugaban ya nemi Ladoja ya yi murabus tun wuri ko a tsigesa.

Cif Ladoja ya ke fadawa Manema labarai wannan a Garin Ibadan Ranar 24 ga Watan Satumban 2019 kamar yadda mu ka samu rahoto. A farkon 2006 ne aka aiko masa takardar shirin sauke shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel