Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya bayyana wani muhimmin aiki da zai samawa matasan kasar nan

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya bayyana wani muhimmin aiki da zai samawa matasan kasar nan

- A taron da ya halarta a birnin New York ranar Litinin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wata muhimmiyar magana

- Shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya zata tattaro matasa su dasa bishiyoyi guda miliyan ashirin da biyar a fadin kasar nan

- Shugaban ya bayyana cewa za ayi hakan ne domin gujewa zaizayar kasa da kuma kwararowar hamada

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce za a tattaro matasan Najeriya domin su shuka bishiyoyi guda miliyan ashirin da biyar a fadin kasar nan, domin gujewa zaizayar kasa da kuma kwararowar hamada.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Litinin dinnan da ta gabata a lokacin da yake jawabi a wajen taron canjin yanayi da aka gabatar a helkwatar majalisar dinkin duniya dake birnin New York.

"Ina so na sanar da cewa gwamnatin Najeriya za ta yi kokari wajen dashen itatuwa domin gujewa zaizayar kasa da kuma kwararowar hamada nan da shekarar 2020," Buhari ya bayyanawa majalisar dinkin duniya.

KU KARANTA: Soja ya kashe kanshi bayan ya shiga gida ya iske matarshi da yake so fiye da kowa a duniya kwance da gardi a gado

"A bangaren ruwa kuwa, gwamnatin Najeriya za ta gina magudanar ruwa (Dam) wanda zai taimaka wajen noman rani da kuma samun wadataccen ruwa. Zamu yi kokari kwarai da gaske wajen domin ganin mutane sun sanya hannun jari a wannan fannin.

"Zamu tattaro matasan Najeriya domin su shuka bishiyoyi guda miliyan ashirin da biyar a fadin kasar nan domin gujewa zaizayar kasa," in ji shugaban kasar na Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel