Ina fatan na rinka sadaukar da dukiya ta tamkar Bill Gates - Dangote

Ina fatan na rinka sadaukar da dukiya ta tamkar Bill Gates - Dangote

Mutumin nan wanda ya fi kowa arziki a nahiyyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana babban fatan da ke cikin zuciyar sa na watan-watarana ya rinka sadaukar da dukiyarsa tamkar hamshakin mai kudin nan na duniya, Bill Gates.

Jaridar The Punch ta ambato Dangote yana fatan shi ma ya rinka fitar da wani babban kaso na dukiyar da ya mallaka ta kimanin dalar Amurka biliyan 9.2 wajen taimakon al'umma a doron kasa.

Dangote wanda alkalumma suka tabbatar da cewa ya fi kowane bakar fata kudi a duniya, ya bayyana wannan fata nasa ne a wani babban taro na bunkasa ci gaba a duniya na Goalkeepers’ event wanda gidauniyar Bill and Melinda Gates ta dauki nauyi a ranar Laraba cikin birnin New York na kasar Amurka.

A yayin taron wanda hamshakan attajiran biyu suka gabatar da jawabai tare da bayyana ra'ayoyi, Dangote ya ce duk ya shafe fiye da shekaru 25 yana gudanar da harkokinsa na kasuwanci a gidauniyar Dangote, ya ce ya zuwa yanzu Bill Gates bai daina burge shi ba a sanadiyar taimako da sadaukar da dukiyar da yake yi kan mabukata a fadin duniya.

A nasa jawaban, Mista Gates ya yi wa Dangote godiya ta musamman a sanadiyar yadda ya kulla alakarsa da wasu gwamnoni na Arewacin Najeriya, inda ya samu damar ganawa da wasu daga cikin kamar gwamnan Aminu Waziri Tambuwal da kuma wasu gwamnoni biyar na Arewacin Najeriya.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar Democrat ta kaddamar da shirin tsige Trump

A wata hira cikin birnin Abidjan na kasar Kwaddebuwa da ta gudana a watan Afrilun da ya gabata tare da wani attajiri irinsa na kasar Sudan, Mo Ibrahim, Dangote ya shawarci matasan zamani masu sha'awar kasuwanci da su mayar da hankali kan harkokin sadarwa da kuma noma.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel