Jam'iyyar Democrat ta kaddamar da shirin tsige Trump

Jam'iyyar Democrat ta kaddamar da shirin tsige Trump

Ta tabbata jam'iyyar adawa ta Democrat ta kaddamar da shirin tsige shugaban kasar Amurka Donald Trump a bisa tanadi na shari'a kan zargin da ake masa na neman gwamnatin kasar Ukraine ta bata sunan abokin hamayyarsa na siyasa.

Kakakin majalisar wakilin kasar wadda ta kasance daya daga cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar Democrat, Nancy Pelosi, ta ce babu makawa shuaba Trump sai ya fuskanci hukunci kan sabawa doka, lamarin da misalta a matsayin yiwa kudin tsarin mulkin kasar karan tsare.

A rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito a ranar Talatar da ta gabata, akwai yiwuwar za a tsige Mista Trump a sanadiyar yunkurinsa na jan hankalin shugaban kasar Ukraine wajen kaddamar da bincike kan dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Democrat, Joe Biden.

Cikin jawabin da Mista Trump ya gabatar a birnin New York, ya zargi 'yan jam'iyyar Democrat da kulla masa tuggu ta bayan fage, sai dai yayin amsa tambayoyin manema labarai ya ce ko kadan ba ya da wani shakku kan barazanar tsige shi.

Takaddamar wannan lamari na zuwa ne a yayin da shugaban kasar Amurka ke zargin 'dan Joe Biden, Hunter Biden, da laifuka na rashawa. Hunter dai ya kasance daya daga cikin manyan ma'aikata masu daukar albashi mafi tsoka a wani babban kamfanin makamashi na kasar Ukraine, Burisma.

Ya zuwa yanzu, Mista Trump na ci gaba da fuskantar matsin lamba a kan ya fitar da bayanai game da wata tattaunawa da ta gudana tsakanin sa da shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ta hanyar wayar tarho.

Sai dai babu ko tantama shugaban na Amurka ya ce sun tattauna dangane da zargin rashawa da ake yiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden da kuma dansa Hunter, wanda ya shafe kimanin shekaru biyar yana aiki da kamfanin na kasar Ukraine.

KARANTA KUMA: Kungiyar kwadago reshen jihar Kebbi ta ki amincewa da N30,000 a matsayin mafi karancin albashi

A yayin da tuni shugaban ya musanta zargin da ake masa na neman bata suna abokin hamayyarsa wanda ya bayyana yunkirin hakan a matsayin bita da kullin siyasa kamar yadda Muryar Duniya ta ruwaito, jam'iyyar Democrat ta yi tsayin daka wajen ganin an tsige shi daga kujerarsa.

Rahotanni na nuni da cewa, akwai yiwuwar binciken zai gamu da cikas daga bangaren Majalisar Dattawan kasar wadda ke karkashin jagorancin jam’iyya mai mulki a kasar ta Republican.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel