PDP za ta tuntunbi shawarar Saraki, Jonathan, Wike da sauransu kan zaben 2023

PDP za ta tuntunbi shawarar Saraki, Jonathan, Wike da sauransu kan zaben 2023

Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin, ya ce nan ba da jimawa ba za su dungunzuma wajen dirfafar tuntube-tuntube da neman shawararin jiga-jigan jam'iyyar domin tumke damarar karbar akalar jagorancin kasar nan a 2023.

Sanata Jibrin kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, ya ce kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, zai nemi shawarar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, da sauran wadanda suka nemi takarar shugabancin kasa a zaben 2019.

Jerin wadanda suka nemi takarar sun hadar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso, gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, tsohon ministan ayyuka na musamman, Tanimu Turaki, tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang da kuma tsohon dan majalisar tarayya mai wakilcin shiyyar Zaria, Datti Baba-Ahmed.

A wata hirarsa da menama labarai cikin birnin Abuja a ranar Talatar da ta gabata, Sanata Jibrin ya ce kwamitin da yake jagoranci zai kai ziyarar neman shawara zuwa ga tsohon shugaban hafsin sojin kasan na Najeriya, Laftanar Janar Aliyu Gusau, tsohon shugaban jam'iyyar Ahmed Makarfi, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Seriake Dickson da kuma sauran mambobin kungiyar.

KARANTA KUMA: Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Ya ce manufar wannan lamari da za su fara aiwatar wa ba ta wuce tumke damarar hambarar da gwamnatin jam'iyyar APC ba domin dawo da martabar PDP wajen sake kaddamar da ita a matsayin babbar jam'iyya ta nahiyyar Afirka.

Ya kara da cewa, tuni wasu daga cikin mambobin kungiyar amintattun jam'iyyar sun ziyarci dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa, lamarin da ya ce hakan wani yunkuri ne na inganta hadin kai domin yiwa jam'iyyar APC dauka daya a zaben 2023 ba tare da farga ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel