Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

A ranar Laraba, 25 ga watan Satumban 2019, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a sanadiyar rashin shugaba Muhammadu Buhari wanda a ya kasance a kasar Amurka domin halartar taron majalisar dinkin duniya karo na 74 a birnin New York.

Osinbajo yayin jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar Villa
Osinbajo yayin jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar Villa
Asali: Twitter

Osinbajo tare da Hajiya Habiba Lawal, wadda ta wakilci sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a zaman majalisar zartarwa
Osinbajo tare da Hajiya Habiba Lawal, wadda ta wakilci sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a zaman majalisar zartarwa
Asali: Twitter

Sashen ministoci da suka halarci zaman majalisar zartarwa
Sashen ministoci da suka halarci zaman majalisar zartarwa
Asali: Twitter

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, manyan kusoshin gwamnati da suka halarci zaman majalisar sun hadar da shugaban ma'aikatan shugaba Buhari, Mallam Abba Kyari da kuma mukaddashiyar shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Mrs Foloshade Yemi-Esan.

Hakazalika ministoci 30 na gwamnatin Buhari sun halarci zaman majalisar a yayin da sakatariyar dindin a ma'aikatar asusun kula da lafiyar dabbobi, Hajiya Habiba Lawal, ta wakilci sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

KARANTA KUMA: Tafkin Chadi: Jawaban Buhari a taron Majalisar Dinkin Duniya

An tattaro cewa, sauran ministocin da basu halarci zaman majalisar ba sun kasance cikin tawagar shugaba Buhari wadda ke halartar taron majalisar dinkin duniya a Amurka. Wasun su kuma na ci gaba da tunkarar badakalar hukuncin diyyar Dala biliyan 9.6 wadda wata kotun Birtaniya ta shimfida a kan kasar nan.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel