FIRS ba ta da kudin da za ta ba Osinbajo Biliyan 90 – Inji Hukuma

FIRS ba ta da kudin da za ta ba Osinbajo Biliyan 90 – Inji Hukuma

Hukumar FIRS mai karbar haraji a Najeriya, ta fito ta karyata rade-radin da ke yawo na cewa ta ba jam’iyyar APC mai mulki biliyoyin kudi a matsayin gudumuwar yakin neman zaben 2019.

A Ranar Litinin, 23 ga Watan Satumba, 2019, FIRS ta bakin Darektan ta na yada labarai, Wahab Gbadamosi, ta musanya zargin cewa ta ba APC wasu kudi ta hannun mataimakin shugaban kasa.

Wahab Gbadamosi ya yi wa tsohon jigon APC wanda ya fara kawo wannan magana watau Timi Frank raddi. Hukumar ta FIRS ta ce sam babu inda ta ba Yemi Osinbajo kudi har Naira biliyan 90.

A jawabin, Gbadamosi ya bayyana cewa: “A cikin shekaru hudu da Mista Tunde Fowler ya yi a matsayin shugaban hukumar FIRS, hukumar ba ta samu Naira biliyan 90 daga gwamnaiti ba.”

FIRS ta nuna idan har ba ta taba karbar Biliyan 90 daga hannun gwamnatin tarayya na abin da ake rabawa domin sha’anin gudanar da aiki ba, babu yadda za su iya ba wani wadannan kudi.

KU KARANTA: 2023: Tinubu ba zai yi mulki ba, wani 'Dan Arewa ne zai cigaba - Yarima

Hukumar ta ke cewa kudin da ta ke karba duk shekara bai kai abin da ake zargin ta da ba APC ba, yayin da ta ke da ma’aikata fiye da 8000 da za ta biya albashi da kuma tarin ofisoshi sama da 150.

Jawabin na makon nan ya na cewa: "FIRS ta na aiki ne a madadin ‘Yan kasa. Ba mu taba harajin mutane, ko kudin aikunmu ko da kuwa majalisar kasa ta sa hannu wajen kasafin wannan kudi.”

A karshe hukumar harajin ta yi kira ga jama’a su yi watsi da wannan zargi da tsohon Sakataren yada labaran na jam’iyyar APC yake yi, inda ta ce ba komai ya ke nema ba sai don a tanka shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel